Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin jagora cewa, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da shugabannin bangarori uku na gwamnati da sauran manyan jami'an gwamnatin Iran inda yayi karin haske kan batutuwa daban-daban da suka hada da batun tattalin arziki na dogaro da kai da tattaunawar da Iran take yi da manyan kasashen duniya kan shirin nukiliyanta musamman batutuwan da wajibi ne a kiyaye su yayin tattaunawar inda ya ce: Babban abin da Amurkawa suke so shi ne kawar da fasahar nukiliyan Iran a daidai lokacin da dukkanin jami'an gwamnati suke fatan ganin an cimma yarjejeniya mai kyau wacce ta ginu bisa adalci wacce za ta yi daidai da maslaha da manufofin Iran.
Tun da fari dai sai da Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi bayani kan watan Ramalana mai alfarma, a matsayinsa na watan takawa da tsoron Allah, inda yayin da yake karin bayani kan nau'oi biyu na tsoron Allah na daidaiku da kuma na zamantakewa cewa yayi: A hakikanin gaskiya tsoron Allah na daidaiku shi ne dai irin wannan kula da kai na koda yaushe da mutum yake yi don kiyaye kansa daga cutarwa mai halakarwa ta nesantar Ubangiji. Wanda tabbas yana da tasiri cikin lamurransa na duniya.
Ayatullah Khamenei ya bayyana cewa ana iya hada tsoron Allah na al'umma tare da batutuwan da suka shafi zamantakewa da kuma tattalin arziki inda ya ce: Tsoron Allah cikin lamurran da suka shafi tattalin arziki, shi ne dai wannan tattalin arziki na dogaro da kai da ka iya kare kasar nan daga matsaloli da suke kunno kai a duniya sakamakon bakar siyasar (manyan kasashen) duniya.
Haka nan kuma yayin da yake sake jaddada jan kunnen da ya sha yi tsawon shekarun da suka gabata na karfafa bangarori daban-daban na kasa don fuskantar matsalolin tattalin arziki da masu tinkaho da karfi na duniya za su haifar, Jagoran cewa yayi: tsawon wadannan shekaru jami'an gwamnati sun yi kokari iyakacin iyawarsu, to amma wajibi ne ya ci gaba da kokari wajen ganin an cimma manufar siyasar tattalin arziki ta dogaro da kai da aka sa a gaba ta amfani da dukkanin damar da ake da su.
Har ila yau Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar mafi yawa daga cikin masanan tattalin arzikin Iran sun yi na'am da wannan siyasa ta tattalin arziki na dogaro da kai din. Haka nan kuma yayin da yake ci gaba da magana kan hakan cewa yayi: Mai yiyuwa ne wasu su ce lalle wannan siyasar abar so ce, to amma babu yadda za a iya cimma hakan. To amma a fili nake fadin cewa lalle bisa la'akari da yanayin da kasar nan take ciki da kuma irin dama da karfin da ake da su, lalle ana iya cimma wannan siyasar.
Daga nan sai Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi karin haske kan wasu daga cikin irin wannan dama da ake da su da za su iya share fagen aiwatar da wannan siyasa ta tattalin arziki na dogaro da kai. Matasa masana masu dogaro da kansu da Iran take da su, shi ne batu na farko da Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da su inda ya ce: Samuwar irin wadannan matasa da suka yi karatu a kasar nan ta samo asali ne albarkacin juyin juya halin Musulunci.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da kimanin daliban jami'oi miliyan 10 da suka gama karatunsu da kuma sama da miliyan 4 da suke ci gaba da karatunsu wanda hakan ya rubanya irin yanayin da ake da shi farko-farkon nasarar juyin juya halin Musulunci sau 25, Jagoran cewa yayi: Irin wannan adadi na matasa da masana da ake da su wani abin alfahari ne na wannan tsari na Musulunci, sannan kuma wata dama ce mai girma da ake da ita.
Batu na gaba da Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da shi, shi ne matsayi na tattalin arzikin Iran inda ya ce: Bisa kididdiga ta duniya, Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana a matsayi na ashirin ne a tattalin arziki na duniya, wanda idan har aka yi amfani da wannan yanayin yadda ya dace akwai yiyuwa a koma ga matsayi na sha biyu na tattalin arziki na duniyan.
Haka nan kuma Jagoran yayi ishara da irin arzikin man fetur da iskar gas da Iran take da shi da sauran albarkatun kasa a matsayin wani bangare na irin wannan karfi da dama da Iran din take da shi da za su taimaka wajen tabbatar da wannan siyasa ta dogaro da kai.
Har ila yau kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da wasu matsaloli da kalubalen da ake fuskanta a cikin gida wadanda za su iya zama karfen kafa ga cimma wannan manufa, don haka sai ya kirayi jami'an gwamnatin da su yi iyakacin kokarinsu wajen magance wadannan matsaloli kamar yadda kuma ya kiraye su zuwa dogaro da irin karfi na matasa da masana da ake da shi a cikin gida don ciyar da kasar gaba; kamar yadda kuma ya kirayi dukkanin al'ummar kasar da su taimaka wa gwamnati wajen cimma wannan manufar. Don haka ne ma ya ce: Ko shakka babu za mu iya yin ayyuka masu girman gaske a fagen tattalin arziki, sannan kuma mu tsallake wannan yanayi mai muhimmanci da sarkakiya da ake ciki.
Wani bangare kuma mai muhimmanci da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya tabo cikin jawabin nasa shi ne batun shirin nukiliyan zaman lafiya na kasar Iran inda ya fara da ishara da wasu batutuwa guda uku masu muhimmanci kafin ya shiga cikin bayani kan sharuddan da wajibi ne a kiyaye su yayin tattaunar da ake yi da manyan kasashen duniya.
Batu na farko shi ne cewa dukkanin abin da Jagoran yake fadi jawaban da yake yi wa al'umma, su ne dai batutuwan da yake gaya wa shugaban kasa da sauran jami'an da abin ya shafa a ganawar da suke yi ta bayan fage. A saboda haka babu gaskiya cikin abin da ake fadi na cewa an yi sassauci kan wasu sharuddan da aka kafa din.
Batu na biyu da Ayatullah Khamenei ya yi ishara da shi a matsayin share fagen bahasin nukliyan shi ne rikon amana, kishi, jaruntaka da kuma riko da addinin na ‘yan tawagar da suke tattaunawar nukiliyan inda yace masu tattaunawar suna da kishin kasa da kuma jaruntaka yayin da suke tattaunawar kamar yadda kuma suke ci gaba da aiki tukuru ba kama hannun yaro.
Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Duk wanda yake da masaniya kan hakikanin abin da ke gudana a wajen tattaunawar, ko shakka babu zai fadi wadannan abubuwan da na fadi. Koda yake mai yiyuwa ne su yi kuskure a wani wajen, to amma a hakikanin gaskiya mutane ne masu riko da addini da kuma kishin kasa.
Bangare na uku da Jagoran yayi magana da su a matsayin share fagen maganar da zai yi kan batun nukiliyan, su ne masu sukan abin da ke gudana a fagen nukiliyan inda ya ce: Ni dai ba na adawa da batun suka, kai ina ganin hakan ma a matsayin wajibi kana kuma abin da zai taimaka. To amma wannan dai wata hakika ce cewa suka ta fi sauki kan aiki. Don kuwa gano aibin wani ya fi sauki amma fahintar irin matsaloli da damuwar da yake ciki ba lamari ne mai sauki ba.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Bai kamata wannan magana tawa, ta hana ci gaba da sukan abubuwan da ake ganin bai dace ba. To amma wajibi ne a fahimci cewa su kansu tawagar da suke tattaunarwa suna da masaniya kan wasu batutuwan da ake sukan, to amma wasu dalilai ne suke sanya a dauki wasu matakan.
Daga nan kuma sai Ayatullah Khamenei ya yi karin haske kan takaitacce tarihin yanayin tattaunawa da Amurka, wanda hakan zai taimaka wajen gudanar da tattaunawa da su.
Jagoran cewa yayi: Batun tattaunawa da Amurka ya taso ne a lokacin gwamnatin da ta gabata yayin da suka turo wakili don neman a fara tattaunawar.
Jagoran ya ci gaba da cewa: A wancan lokacin, wani mutum da ake girmamawa a wannan yankin ya zo wajenmu a matsayin wakili inda a fili ya fadi cewa shugaban kasar Amurka ya bukace shi da ya tafi Tehran ya gabatar musu da bukatar Amurkawa ta tattaunawa. A lokacin an gaya masa cewa lalle muna son a magance wannan batu na nukiliya ta hanyar amincewa da Iran a matsayin wacce ta mallaki fasahar nukiliya, sannan kuma cikin watanni shida a dauke (mana) takunkumin. Koda yake mun gaya wa shi wannan wakilin cewa mu dai ba mu nitsu da Amurkawa da kuma maganganunsu ba. To amma saboda jajircewar wannan wakilin muka amince da hakan, da cewa bari mu sake gwada Amurkawan. Don haka aka fara tattaunawar.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: A dukkanin wata mu'amala ta diplomasiyya, akwai fagage guda biyu wadanda wajibi ne a yi la'akari da su. fage na asali ne fagen na hakika da gaskiya da kuma aiki. Don haka jami'an diplomasiyya da siyasa wadanda sune masu kula da wadannan abubuwa, suna aiki ne wajen tabbatar da manufa da amfani na kasa.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Rashin karfin kowace kasa a fagen farko, yana yin tasiri da kuma takaita ayyukanta a fage na biyun. A saboda haka ne ta shiga wannan fagen da wani karfi da kuma nasara mai muhimmancin gaske wanda shi ne karfin fasahar tace uranium kashi 20 cikin dari.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar dukkanin kasashen da suka mallaki fasahar nukiliya sun ki su sayar wa Iran da makamashin uranium da aka tace kashi 20 cikin dari don amfani cibiyoyin nukiliyan Tehran, kai hatta ma suna kokarin hana mu saye daga wasu kasashen na daban. Amma sai ga shi matasanmu sun samar da wannan makamashi.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Baya ga taceccen uranium kashi 20 cikin dari, har ila yau kuma akwai wasu nasarorin da muka samu wadanda a hakikanin gaskiya sun taimaka wajen tsayin dakan tinkarar matsin lambar da Iran take fuskanta. Daga nan ne Amurkawa suka fahimci cewa lalle takunkumin da suka sanya wa Iran bai yi irin tasirin da suke so ba. Don haka wajibi ne su samo wata hanyar ta daban.
Haka nan kuma Ayatullah Khamenei yaci gaba da karin haske kan batun shakkun da Iran take da shi kan Amurka inda ya ce: Duk da hakan, amma dai mu a shirye muke idan har Amurkawa za su tabbatar wa wannan wakilin za su girmama magana da kuma alkawarin da suka yi, za mu sassauto kan wasu abubuwan don kuwa idan har za a gudanar da tattaunar da ta dace da hankali ai daman wajibi ne a sassauto kan wasu abubuwan. To amma tun ba a je ko in aba suka fara wannan rashin cika alkawari na su.
Haka nan kuma yayin da yake bayanin cewa yarjejeniya mai kyau dai a mahangar Iran ita ce yarjejeniya da aka cimma ta cikin adalci da girmama juna, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa yayi: A yayin tattaunawar, Amurkawa sun yi alkawarin cewa cikin watanni shida za su dage takunkumin, suka zo suka mai da shi shekara guda, daga nan suka ci gaba da neman wuce gona da irin su da neman tattaunawa ta tsawon lokaci kai har ma suka fara barazanar kara sanya takunkumin. Suna ta magana kan batun kawo hari na soja da sauransu.
Don haka sai Jagoran ya ce: Dubi da kuma tuntuni cikin wadannan bukatu na Amurka yana nuni da cewa manufarsu ita ce tumbuke tushen ilimi da fasahar nukiliya da ake da shi da mai she shi wani yanayi kawai na boge maras amfani.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da bukatar da Iran take da ita na samar da wutar lantarki na nukiliya da ya kai mega watt dubu 20, Ayatullah Khamenei cewa yayi: Wadannan mutane saboda wannan manufa da suke da ita na kawar da fasahar nukiliya da muke da ita, sun yi ta kokari da kuma ci gaba da matsin lambarsu wajen ganin sun kara tabbatar da wadannan takunkumin.
A ci gaba da wannan bayani nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da wani bangare na wannan tattaunawar wanda shi ne bukatar da Amurka take da ita ga cimma yarjejeniyar nukiliyan.
Jagoran ya bayyana cewar: Idan har za su iya cimma wannan manufa ta su ta hanyar tattaunawa, lalle sun cimma wata babbar nasara, don kuwa al'ummar Iran ma'abota neman ‘yanci sun mika kai, sannan kuma sun yi nasara a kan kasar da za ta iya zama abin koyi ga sauran kasashe. Dukkanin alkawurra da maganganun da suke yi don cimma wannan manufar ce.
Haka nan kuma yayin da yake sake jaddada bukatar Iran tun a farkon tattaunawar har zuwa yau, Jagoran cewa yayi: Mu dai tun da fari mun fadi cewa abin da muke so shi ne a dage mana takunkumin zaluncin da aka sanya mana, kuma a shirye muke mu ma mu ba da wani abin, amma da sharadin ba za a dakatar da aikin nukiliyanmu ba sannan kuma ba za a cutar da shi ba.
A ci gaba da jawabin nasa, Ayatullah Khamenei yayi karin haske dangane da sharuddan da Iran ta kafa da babu yadda za a iya watsi da su. Batu na farko da Jagoran yayi ishara da shi shi ne fadinsa cewa: Mu dai sabanin abin da Amurkawa suke fadi na sanya iyakoki na shekaru 10 zuwa 12, lalle ba mu amince a hakan ba. Mun sanar da su kan iyakoki da shekarun da muka amince da su.
Jagoran ya bayyana ci gaba da ayyukan bincike da ci gaban ayyukan nukiliya hatta a lokacin da aka tsara din shi ne sharadi na biyu da Iran ta kafa inda ya ce: Suna fadin cewa tsawon shekaru 12 kada ku yi wani abu. To amma wannan wata magana ce ta nuna karfi sannan kuma karin kuskure.
Yayin da yake magana kan sharadi na ukun da ba za a taba amincewa a ketare shi ba, Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa yayi: Wajibi ne a dage takunkumi na tattalin arziki da kudi da bankuna wadanda kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya da majalisa da kuma gwamnatin Amurka ta sanya mana daga lokacin da aka sanya hannu kan yarjejeniyar, sannan sauran takunkumin cikin wani lokacin da za a tsara da yayi daidai da hankali.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Amurkawa suna gabatar da wata hanya mai ban mamaki da sarkakiya kan yadda za a dage takunkumin, wanda babu tabbacin abin da za a samu a cikinsa. To amma mu a fili mun gaya musu mahangarmu.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Bai kamata a damfara dage takunkumi da aiwatar da nauyin da ke kan Iran ba. Kada ku ce mana ku sauke nauyin dake wuyanku daga nan idan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta shaida shi kenan sai a dage muku takunkumi. Mu dai ba za mu taba amincewa da hakan ba.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: wajibi ne a aiwatar da aikin dage takunkumin daidai lokacin da Iran ta fara aiwatar da nauyin da ke wuyanta.
Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Mu dai ba za mu amince da damfara fara aiwatar da nauyin da ke wuyan daya bangaren da muke tattaunawa da shi da rahoton hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ba, don kuwa a lokuta da dama wannan hukumar ta sha tabbatar da cewa ita din nan ba ta ‘yancin kai sannan kuma ba ta da adalci cikin ayyukanta. Don haka hankalinmu bai kwanta da ita ba.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Suna fadin cewa "wajibi ne hankalin hukumar nukiliyan ya nitsu" wannan wace magana ce da ta saba wa hankali. Ta ya ya za a ta samu nitsuwar, face sai ta bi dukkanin lunguna na kasar nan tana bincike.
Ayatullah Khamenei ya bayyana rashin amincewa da binciken da ya saba wa yadda aka saba gudanarwa da kuma gudanar da tambayoyi wa jami'ai da masanan Iran da kuma binciken sansanonin soji a matsayin wani sharadin da Iran ta kafa.
A fili Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: A Iran dai kowa da kowa ciki kuwa har da ni kai na, gwamnati, majalisar, hukumar shari'a, cibiyoyin tsaro da na soji da sauran cibiyoyi kowa yana son a cimma yarjejeniya mai kyau, yarjejeniyar da ke cike da kare mutumci wacce kuma ta yi daidai da maslaha ta kasa.
Jagoran ya ce: Duk da cewa muna son ganin an dage takunkumi, to amma ta wani fagen muna ganin hakan a matsayin wata dama. Don kuwa hakan zai ba mu damar kara ba wa karfi na cikin gida da muke da shi karin kulawa.
Kafin jawabin Jagoran dai sai da shugaban kasar Iran Hujjatul Islam wal muslimin Hasan Ruhani ya gabatar da jawabinsa inda yayi karin haske kan batutuwa daban-daban da suka shafi kasar Iran da kuma irin ayyukan da ake ci gaba ga gudanarwa.
3317960