IQNA

Za A Kafa Cibiyar Malaman Addinin Musulunci Na Afirka A kasar Morocco

22:36 - June 28, 2015
Lambar Labari: 3320696
Bangaren kasa da kasa, za a kafa wata cibiya ta malaman addinin muslunci na nahiyar Afirka mai suna cibiyar muslunci ta sarki Muhammad ba biyu a kasar Morocco.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ina cewa, a kasar Morocco  za a kafa wata cibiya ta malaman addinin muslunci na nahiyar Afirka mai suna cibiyar muslunci ta sarki Muhammad ba biyu na kasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa babbar manufar kafa wannan cibiya karkashin sarki Muhammad na biyu dai ita ce, hada kan dukkanin malaman nahiyar Afirka a wuri guda, domin aiki tare wajen fuskantar kalu bale da ke a gaban mabiya addinin muslunci.

Daga cikin irin wannan kalu bake kuwa har da yadda ake samun yaduwar ayyukan ta’addanci a cikin kasashen musulmi, wanda kuma hakan yak an bar mummunan tasiria  tsakanin musulmi musamman ma matasa daga ciknsu, wadanda ba su da masaniya kan addini.

Aikin da cibiyar za ta mayar da hankalia  kansa, bayan ilmantarwa, akwai kuma wayar da kai dangane da sanin hakikanin addini muslunci, da kuma sanin yadda ya kamata musulmi su tunkari mumanan akidu na ta’addanci da ake shigo da su a cikin musulmi a halin yanzu.

Hakan kuma dukaknin bangarorin na malaman kasashen Afika da na Morocco za su aiki tare domin yada al’adun muslunci da kuma koyarwarsa tsakanin sauran al’ummomin nahiyar da bas u da masaniya wannan addini a cewar bayanin.

3320338

Abubuwan Da Ya Shafa: Moroco
captcha