IQNA

An Gudanar Da Bangare Na Karshe Na gasar Kur’ani A Kasar Senegal

23:56 - June 29, 2015
Lambar Labari: 3321186
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da bangare na karshe a gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasa baki daya abirnin Dakar na kasar Senegal tare da halartar makaranta da mahardata daga fadin kasar.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Dunya Bulteni cewa, a jiya an kammala gudanar da bangare na karshe a gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasa baki daya  abirnin Dakar na kasar Senegal tare da halartar makaranta da mahardata daga fadin kasar da suka fito daga yankuna 14 na kasar.

 

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasa mai matukar muhimmanci ce a kasar wadda ake gudanarwa a kowaece shekara sau guda a babban dakin taro na birnin mai kujeru 800, kuma ana gudanar da ita ne a cikin watan domin sabon albarkcin wannan wata mai alfarma wanda a cikinsa aka safkar da kur’ani mai tsarki.

Fitattaun makaranta da maharda daga sasa na kasar sukan halarta, inda suke nuna irin baiwar da Allah madaiukakin sarki ya yi musu ta fsuakr karatu da kuma hardar kur’ani mai tsarki, kamar yadda akan gayyaci alkalai daga kasashen ketare musamman ma na larabawa domin yin alkalnci a gasar.

 

Akan bayar da tukuici na dalar Amurka dubu 20 ga wanda ya zo na daya, sai kuma dala dubu 10 ga wanda ya zo a matsayi na biyu, sai kuma dala dubu 6 ga na uk, sai kuma dala dubu 4 ga na wanda yay a zo na hdu.
3320975

Abubuwan Da Ya Shafa: senegal
captcha