IQNA

An Fara Gudanar Da Gasar Hardar Kr’ani Mai Tsarki A Birnin Qods

20:14 - July 01, 2015
Lambar Labari: 3322220
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar hardar kr’ani mai tsarki a birnin Qods tare da halartar mahardata daga yankuna da daman a Palastinu.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Safa cewa, Sheikh Abdulrahman Bukairat wanda shi ne ya tsara gasar ya bayyana cewa, an shirya wannan gasa ne tare da halartar mahardata daga yankuna da daman a Palastinu domin su kasance bangare na masu gasar.

Ya kara da cewa akwai bangarori biyu na gasar da suka hada da na maza da kuma na mata, inda dukkaninsu suke yin iyakcin kokarinsu tare da nuna wa sauran matasa cewa za su iya yin koyi da su wajen karatu da kuma hardar kur’ani mai tsarki.

Malamin ya ci gaba da da cewa akwai malamai da aka gayyata da suke gudanar da alkalnci a gasar, wadanda su ma sun fito daga yankunan  gabacin birnin da kuma wasu yankunan gabar yamma ta kogin Jordan.

Baabbar manufar gasar dai it ace kara jawo hankulan matasa domin su mayar da hankali ga lamarin kur’ani mai tsarki da kuma koyarwarsa, wanda kuma ko shakka babu gudanar da gasar yanan karfafa gwiwar matasa wajen ganin sun shiga dominb kada a bar su a baya.

Y ace a wannan karon abin ya yi armashi fiye da ydda aka yi a sauran lokutan da suka gabata, bisa la’akari da kara samun gogewa da aka samu a tsakanin masu gudanar da kaatun da kuma masu shirya gasar, wadanda su ma suna kara samun ci gaba a wannan fage.

Za a bayar da kyautuka na kudade dalar Amuka dubu 5 da 4 da 3 ga wadamnda suka zo na daya, na biyu, da kuma na uku, sai kuma na hudu har zuwa na goma za su samu kyatat dala 200 kowane daga cikinsu.

3321749

Abubuwan Da Ya Shafa: palestine
captcha