Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin nsadarwa na yanar gizo na jaridar kasar Qatar da Al-arab cewa, cibiyar RAF ta kasar Qatar tana gudanar da ayyukan jin kai a kasshen Afirka musamman a kasar ta Somalia inda take daukar nauyin ayyukan alhairi musamman ma a cikin watan Ramadan a cikin kasashen,
Daga cikin ayyukan da za su gudanra halin yanzu har da gina cibiyoyi na koyar da hardar kur’ani mai tsarki guda 30 a cikin wadannan kasashe, inda ahalin yanzu sun ware kudi har Riyal miliyan 2 da kuma 407 domin gudanar da wannan gagarumin aiki na alkhari.
Masu gudanar da shirin sun ce za a gina wadannan ciyoyi guda 30 ne acikin wadannan kasashe, tare da bas u dukkanin abubuwan da suke bukata na aiki, za a gida guda 25 a cikin kasar Brundi, sa kuima guda 5 a cikin kasar Somalia.
Kowace daya daga cikin cibiyoyin za ta lakume kudi har riyal dubu 76, kuma hakan kowane daga cikin cibiyoyin zai kwashi dalibai 80 maza da mata domin koyar da su hardar kur’ani mai tsarki.
3322011