IQNA

Ana Tilasta Daliban Makarantar Sakandare Musulmi Zuwa Majami’a A Kenya

23:10 - July 02, 2015
Lambar Labari: 3322412
Bangaren kasa da kasa, jami’an wata makarantar sakandare a yankin Mumbasa na kasar Kenya suna tilasta wa daliban makaratar musulmi zuwa wata majami’a da ke cikin makarantar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Duniya Bulletin cewa, iyayen yara musulmi suna nuna rashin amincewa bayan da jami’an wata makarantar sakandare a yankin Mumbasa na kasar Kenya suka tilasta wa yaransu zuwa wata majami’a da ke cikin makarantar domin gudanar da ibadar kirista.

Abdulsamad Nasir dan majalisar dokokin kasar ne daga wannan yanki, ya bayyan acewa ba su taba amincewa da wannan mataki na tilasta yaransu su tafi majami’a ba, domin sub a mabiya addinin kirista ba ne, kuma hakanh ya yi hannun riga da dokokin kasar da suka halasta kowane dan kasa yin addinin da ya ga dama.

Y ace za su dauki dukkanin matakan da suka dace domin fuskantar wannan lamari, domin kuwa ya saba wa abin da suka amince da shi kamar yadda ya sabawa dokokin kasa da ma dukkanin dokoki na duniya, kuma ba su tbas uari hakkinsu ya salwanta ba suna ji suna gani.

A lokutan baya wata makaranta ta yi irin wannan a cikin kasar ta kenya, inda iyayen yara suka kai kara  agaban kotu domin neman abi musu hakkinsu na yan kasa, wadanda suke hakkin su yi addinin da ske bukata, amma kotu ta tabbatar da cewa bai kamata ‘yan mata su je makaranta da hijabi ba.

3322065

Abubuwan Da Ya Shafa: kenya
captcha