IQNA

Majalisar Malam Kasar Sudan Ta Haramta Shiga Kungiyar Daesh

23:46 - July 07, 2015
Lambar Labari: 3325751
Bangaren kasa da kasa, majalisar malamain addinin muslunci ta kasar Sudan ta fitar da fatawar haramta shiga kungiyar yan ta’adda ta Daesh a shar’ance.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-nailin cewa, Sheikh Muhammad Usman Saleh babban sakataren majalisar malan Sudan ya bayyana  cewa, sun fitar da fatawar haramta shiga kungiyar yan ta’adda ta Daesh a shar’ance ga musulmin kasar.

Ita ma a nata bangaren gwamnatin ta Sudan ta dauki kwararan matakai dangane da matasan kasar da ke yin tafiya zuwa kasar Turkiya, inda sukan shiga cikin kasar sham a domin yin yaki a sahun ‘yan ta’adda na Daesh.

An bayar da rahoton cewa, gwamnatin kasar ta Sudan ta dauki wadannan matakai ne sakamakon yadda daliban jami’a a kasar suke shiga kungiyar ta’addanci ta IS, kuma suke ta yin tafiya zuwa Syria domin yin yaki tare da sauran ‘yan kungiyar, inda sukan tafi santanbul daga can kuma su shiga kasar ta sham, inda gwamnatin ta Turkiya ta bude iyakokinta ga ‘yan ta’adda daga ko’in cikin fadin duniya domin su shiga cikin kasar ba tare da wata matsala ba.

A cikin ‘yan kwanakin da suka gabata ne jami’an tsaron kasar Sudan suka samu nasarar dawo da wasu daga cikin matasan kasar ‘yan jami’a da suka tafi santanbul da nufin shiga, domin abin da suka kira yaki a cikin sahun ‘yan kungiyar ta yan ta’add.

3325439

Abubuwan Da Ya Shafa: sudan
captcha