IQNA

An Giramma Wadanda Suka Shirya Gasar Kur’ani Mai Tsarki ta Dubai

23:50 - July 07, 2015
Lambar Labari: 3325753
Bangaren kasa da kasa, an girma mutanen da suka dauki nauyin shiryawa da kuma gabatar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta birnin Dubai.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na gasar cewa, a jiya ne aka gudanar da taron girma mutanen da suka dauki nauyin shiryawa da kuma gabatar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta birnin Dubai tare da halartar kwamitin gasar da kuma alkalaisakamakon kokarinsu.

A gasar dai dan kasar Bangaladash ne ya samu matsayi na daya, kamar yadda wani dan kasar Mauritaniya ya samu mataki na biyu, yayin da kuma wakilin Iran agasar Muhammad HussainBehzadfar ya zo mataki na uku a gasar.

Wanannmatsayi na uku wanda aka bayar da shi ga mutumin da ya fi kyautata sautia  gasar shi ne wanda Muhamamd Hussain Behzadfar dan kasar Iran ya samu, wanda ya zama a bin fahari ga dukkanin al’ummar jamhuriyar Muslunci ta Iran baki daya.

3325356

Abubuwan Da Ya Shafa: dubai
captcha