Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-sharq ta kasar Qatar cewa, yanzu haka an ware kudi Riyal miliyan 10 domin gudanar da aikin buga kur’ani da za a rarraba a wasu kashe 62 na duniya.
Daya daga cikin cibiyoyin ayyukan jin kai na kasar Qatar ta ce za ta buga tare da yada kwafi dubu 50 na alkur’ani, amma bisa sharadin a tarjama dubu 25 daga cikin su cikin harsunan Italiyanci, Jamusanci, Portugal da kuma Spaniyanci.
A kan haka Ayid Bin Dasan Alqahtani shugaban bababr cibiyar bayar da agaji ga al’ummomi mabukata ya bayyana cewa, suna son ganin sun gudanar da wannan aiki ne da nufin isa da sakon kur’ani mai tsarki zuwa ga sassa na duniya, musamman ma wadanda ba su da masaniya kan kur’ani.
A bangare guda kuma ya bayyana cewa suna gudanar da ayyuka na jin kai a wasu daga cikin kasashen anhiyar Afirka, da nufin tallafawa mutane marassa galihu, musamman ma da abubuwa na tallafin rayuwa, kamar yadda sukan gina musu cibiyoyin addini da koyar da karatun kur’ani.
Ya kara da cewa cibiyar tana ci gaba da kara fadada ayyukan da ke gudanarwa da nufin ganin an samu yaduwar ilmin kur’ani tare da ayyukan agaji na tallafin masarufin rayuwa alokaci guda, ga al’ummomi mabukata.
3325638