Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na QAF cewa, an gudanar da wannan babban taron karatun kur’ani mai tsarki ne a babban masallacin Quds da ke birnin na Capetown da ke kasar Afirka ta kudu.
Bayanin ay ci gaba da cewa an gudanar da wannan taro ne na karatun kur’ani mai tsarki a karkashin babbar cibiyar muslunci ta kasar wadda take wannan birni, tare da halartar makaranta daga Masar, Sudan, Iraki da kuma Malayzia da suka yi karatu a wurin.
Wannan taro dai ya samu karbuwa a tsakanin mabiya addinin uslinci na kasar, daga cikin masu karatun kuwa har da fitaccen makarancin nan na kasar Masar Mahmud Muhammad Abdulwahab Al-tantawi, sai kuma dan Iraki makaranci Rafei Alamiri.
Hakan nan kuma daga cikin wadanda suka halarci gasar kuma suka yi karatu akwai Muhammad Sefr dan kasar Sudan, sai kuma Farajallah Shazeli shi ma daga Masar, bayansa kuma akwai Bin Haq dan kasar Malayzia wanda ya yi karatu a wurin mai ban sha’awa.
Wannan babban taro na karatun kur’ani mai tsarki a kasar Afirka ta kudu akan bayar da kyautuka ga wadanda suka nuna kwao kamar dai yadda aka saba yi a kowace shekara, da hakan ya hada da alluna na ban girma.
3328647