Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ma’alumah cewa, wannan hari yay i sanadiyyar mutuwar mutane akalla 120 da kum ajikkatar 130 a yankin, yayin da wasu kimanin 20 kuma suka bata.
A nasu bangaren Jami’an sojin kasar Iraki sun sanar da halaka adadi mai yawa na ‘yan ta’addan IS a yau a garin Mausil na kasar Iraki, da suka hada har da wasu daga cikin manyan kwamandojin kungiyar.
Kamfanin dillancin labaran saumariyyah News daga kasar ta Iraki ya bayar da rahoton cewa, rundunar sojin kasar ta Iraki ta bayyana hare-haren da jiragenta na yaki suka kaddamar da kan wani dandazon mayakan ‘yan ta’addan is a garin mausil da cewa babbar nasara ce, domin kuwa a cewar bayanin, daga cikin wadanda aka kashe akwai wasu daga cikin manyan na hannun damar jagoransu.
Wasu rahotanni kuma sun ce kotu ta yanke hukuncin kisa kan mutanen da suka tayar da bama-bamai a yankin Bani Sa’ad a cikin gundumar Dayali wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, tuni dai jami’an tsaron Iraki suka kame maharan tare da gurfanar da su a gaban kuliya, kuma kotu ta ce za a kashe su ne a bainar jama’a, kuma a daidai wurin da suka tayar da bamai-bamai suka kashe fararen hula.
3329152