Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Iraq Press cewa, a jiya ‘yan ta'addan Daesh masu da'awar addini sun yanka daya daga cikin manyan malaman 'yan Sunnah na kasar Iraki Sheikh Najmuddin Kan'an Al-jaburi, kuma babban limamin masallacin Al-Humaid da ke garin Mausil, bayan da kungiyar ta kafurta shi saboda yana saba wa umarninta.
Bayanin ya ci gaba da cewa yan ta’addan sun sace Sheikh Najmuddin Kan'an Al-jabur malamain ne daga wani kauye mai suna Mashirfah a yammacin birnin Mausil, inda suka kawo birnin suka harbe shi da bindiga abainar jama’a.
Wannan dai ba shi ne karon farko da suke aiwatar da irin wannan aiki na dabbanci ba, domin kuwa kafin nan sun kashe wasu daga cikin malamai a birnin saboda rashin bin umarninsu kamar dai yadda suke shedawa.
Adadain malaman da suka kashe a Mausil ya kai kimanin 15 yayin da kuma wasu kimanin 40 suke a hannunsu kuma ba a san makomarsu ba.
3331913