Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alwatan cewa, a lokacin da yake zantawa da wannan kafa Abbas Shauman mataimakin babban malamin cibiyar Azhar ya bayyana cewa ba su kafirta musulmi kuma mazhabar shi’a daya ce daga cikin mazhabobin muslunci da ake da su a duniya.
Abbas Shauman ya ci gaba da cewa akwai masu daukarvtsauraran matakai na kafirta wani bangare na al’ummar musulmi, alhali wannan ya saba wa koyarwar wannan addini, musamamn masu kafirta mabiya mazhabar shia.
Ya ce Mazhabar shi’a Imamiyyah day ace daga cikin mazhabobin addinin muslunci, kuma yana da kyau a kawo karshen kallon da ake yi musu a matsayin wajen addini, domin hakan abbabn kure ne wanda ke cutar da musulunci da musulmi ko sun sani ko ba sani ba.
Dangane da kiran da Ahmad tayyib shugaban cibiyar ta Azahar ya yi kan gudanar da zama tsakanin manyan malaman addini daga dukkanin bangarori, ya bayyana hakan da cewa shawara mai kyau, domin za ta taimak wajen kara kusanto da fahimtar malaman addinin muslunci.
Ya ci gaba da cewa babu amfani wani bangare na shi’a ko sunna ya wulakanta daya bangaren saboda banbancin fahimta kan wasu lamurra wadanda ba su ne ainahin addini ba, su wane bangare ne da bai kai matsayin ya zama addini ba, amma kuma an abata lokaci a kansa.
Sheikh Muhamamd Shaltut tsohon malamin cibiyar Azhar, a cikin sheakara ta 1378 a ranar haihuwar Imam Sadeq (AS) a gaban dinbin malaman shi’a da na Hanafiyyah, malikiyyah, Hambaliyyah Shafiyya ya fito ya yi ta maza ya bayar da fatawar halascin bin amzhabar Ahlul bait (AS).
3332613