IQNA

Ya Zama Wajibi A Kafa Kawance Na Kasashen Larabawa Da Musulmi Domin Yaki Da Takfiriyyah

22:29 - July 25, 2015
Lambar Labari: 3335069
Bangaren kasa da kasa, Sheikh Na’im Kasim ya bayyana cewa ya zama wajibi a hada karfi da karfe domin yaki da kungiyar ‘yan ta’addan takfiriyyah.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na SANA cewa, Sheikh Na’im Kasim mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah ya bayyana cewa, idan da Iran da Syria ba su taimaka ma Hizbullah ba, to da kungiyar ba ta iya samun nasarar da ta samua  yakin kwanaki 33 da Isra’ila ba.

Ya ci gaba da cewa Amurka da kawayenta da suka shirya makirci rusa kasar Syria a yanzu sun fahimci cewa hankoronsu an kifar da gwamnatin wannan kasa ba a bu ne mai yiwuwa ba, kuma ba za su taba samun nasara a kan wannan mummunar bakar manufa ta su ba.

Sheikh Na’im Kasim y ace ya zama wajibi a kan sukkanin al’ummomin yanki da su zama cikin fadaka su gane cewa hada kai da yin aiki tare domin tunkarar hadarin da keg aba shi ne mafita, domin kuwa hakan shi ne babban gishikin nasar gwagwarmaya.

Dangane da irin barazanar da Isra’ila ta ke yi kuwa, ya bayyana cewa gwamnatin yahudawan sahyuniya ba ta taba zama ta hut aba, kuma ba za ta yi hakan ba, matukar dai akwai gwagwarmaya ta neman yanci a cikin kasashen larabawa, domin hakan ne abin da zai kawo karshenta.

Ya ce Syria ba ta kasance ba face wani bangare mai muhimmanci na gwagwaraya a yankin gabas ta tsakia, kuma kasar Saudiyya ta kasance kan gaba wajen kashe kudade da nufin rusa wanann kasa ta yadda Isr’aila za ta sarara, amma kuma kudin da ta kashe za su zae mata asara.

Sheikh Kasim ya jaddada cewa ya zama wajibi a kafa wata hgamayya ta al’ummomin larabawa da musulmi domin tunkarar barazanar yan ta’adaddan takfiriyyah a yankin baki daya.

Tun jiya ne dai aka fara gudanar da taon yaki da ta’addanci na kasa da kasa a birnin Damascus na kasar Syria, tare da halartar vmanyan alaai da masana daga kasashen duniya.

Wanda ya wakilci Iran a taron shi ne Ali Jannati kuma ministan yada la’adu na jamhuriyar muslunci, haka nan kuma ministan yada labaran Syria Umran Zu’uzi shi ne ya wakilci shugaban kasar, an samu halartar masana daga kasashen Rasha, China, Iran, Turkiya, Afghanistan, Pakistan, Masar, Lebanon, Iraki, Algeriya, Morocco, Bahrain, Jordan, Sudan, saudiyyah, Tunisia, Cyprus, England, Jamus da kuma Kuwait, an bude taron ne jiya mai take gudunmawar kafofin yada labarai wajen yaki da ta’addanci.

3332574

Abubuwan Da Ya Shafa: Hezbollah
captcha