IQNA

Jaridar Guardian Ta Kasar Birtaniya Ta Tona Asirin Da Tsakanin Turkiya Da Daesh

23:54 - July 27, 2015
Lambar Labari: 3335985
Bangaren kasa da kasa, jaridar Guardian ta kasar Birtaniya ta tona asirin da ke tsakanin gwamnatin kasar Turkiya da kuma ‘yan ta’adda Daesh.


Kamfanin dillancin labaran iqn aya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Press TV cewa, jaridar Guardian da a ke bugawa a kasar Birtaniya ta tona asirin da ke tsakanin gwamnatin kasar Turkiya da kuma ‘yan ta’adda ISIS da suke gudanar ayyukan ta’addanci a yankin.

A nasu bangaren masana da ma wasu daga cikin ‘yan siyasa da kuniyoyin lauyoyi masu zaman kansu a kasar ta Turkiya, suna bayyana cewa gwamnatin kasar ba za ta iya wanke kanta daga abin da ya faru ba, domin kuwa tun farko ta tafka babban kure na siyasa, inda ta zake wajen mara baya ga ‘yan ta’adda a Syria, domin cimma wata manufa ta siyasa  akan gwamnatin Syria.

Masu wannan ra’ayi a kasar ta Turkiya suna ganin cewa, bin irin wannan salo da gwamnatin Erdogan ke yi, ya cutar da kasar ta fuskoki da dama, musamman ta fuskar siyasar waje, haka nan kuma ya cutar da ita kanta jam’iyyar tasa mai mulki, kamar yadda kowa ya sheda a sakamakon zaben ‘yan majalisar dokoki da ya gabata, kamar yadda kuma hakan zai cutar da sha’anin tsaron kasar a lokacin da ‘yan ta’addan da gwamnatin kasar ke mara wa baya domin rusa kasashen Iraki da Syria suka juyo kanta, wanda kuma shi ne abin da aka fara gani a halin yanzu.

Zanga-zangar la’antar gwamnatin Erdogan a cikin kasar Turkiya da ke dora alhakin hare-haren ta’addanci na kunar bakin wake a kan siyasar gwamnatinsa, na ci gaba da bazuwa a cikin biranan kasar tun daga ranar Talatar da ta gabata, wanda kuma ci gaba da yin amfani da karfin tuwo wajen murkushe zanga-zangar ta PKK da sauran ‘yan adawa, ya kara rura wutar bazuwarta zuwa wasu sauran yankunan kasar, lamarin da idan ya ci gaba a hakan, zai iya barin mummunan tasiri ga makomar jam’iyya mai mulki a kasar a siyasance.

3335825

Abubuwan Da Ya Shafa: daesh
captcha