IQNA

An Rufe Wasu Daga Cikin Masallatai A Kasar Kamaru

21:22 - July 28, 2015
Lambar Labari: 3336430
Bangaren kasa da kasa, mahukunta a kasar Kamaru sakamakon dalilai na tsaro sun sanar da rufe wasu daga cikin masallatai da cibiyoyin addini a rewacin kasar na wani dan lokaci.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga jaridar Los Ageles Times cewa, bayan sanar da daukar matakin rufe wasu daga cikin masallatan a kasar kamaru hakan ya fuskanci kakakusar daga wasu mutanen kasar.

Alaji Haman dattijo dan shekaru 70 da haihuwa daga garin Marwa ya kirayi mahukuntan kasa da su sake yin nazari dangane da wannan mataki da suka dauka, domin kuwa a cewarsa hakan bai dace ba.





Bayan sanar da wannan bayani na mahkuntan kasar,a  ranar Lahadin da ta gabata na rufe masallatai da wasu daga cikikin cibiyoyin addinin muslunci da ke yankunan arewacin kasar.

Mahukuntan an kamaru sun danganta hakan ne da irin barazanar da ake fuskanta na hare-hare daga kungiyar yan ta’adda ta Boko Haram a cikin wadannan yankuna.

Kimanin kasha 20 cikin dari na mutane miliyan 20.5 da ke kasar mabiya addinin muslunci ne, wadanda akasarinsu kuma suna zaune a yankunan arewacin kasar .

‘Yan ta’addan Boko haram suna yin koyi ne da kungiyar Taliban a kasar Afghanistan, tare da ikirarin kafa daular muslunci a Najeriya, kasa mafi girma ta fuskar tattalin arziki ta daya wajen hakar amn fetur a nahiyar Afirka.

Lamarin da ya zuwa ya zuwa yanzu ya shafi wasu daga cikin kasashen da suke makwabtaka da kasar, musamman Chad, Nijar, da kuma jamhuriyar ta Kamaru.

3336158

Abubuwan Da Ya Shafa: kamaru
captcha