IQNA

An Yanke Hukuncin Daure Wasu Masu Goyon Bayan Daesh A Ethiopia

23:56 - August 04, 2015
Lambar Labari: 3339006
Bangaren kasa da kasa, kotun kasar Ethiopia ta fitar hukunci kan wasu mutane 17 na dauri a gidan kaso bisa zarginsu da mara baya ga kungiyar ta’addanci ta Daesh.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ae24 cewa, a jiya kotun kasar Ethiopia ta daure mutane 17 na  dauri a gidan kaso bisa zarginsu da mara baya ga ayyukan neman kafa gwamnatin musulunci karkashin kungiyar ta’addanci ta Daesh a kasar.

Wannan kotu ta fitar da wannan hukunci ne bayan gurfanar da mutanen tare da gabatar mata da dalilai da ke nuni da cewa suna da alaka da kungiyar, daga cikinsu har da dan jaridada aka daure shi shekaru 7 a gidan kaso.

Wadannan mutane dai ba su amince da wannan hukunci na kotu ba, kamar yadda kuma bas u amince da abin da ake zarginsu da aikatawa ba, na cewa suna hankoron mayar da kasar kiristoci zuwa kasar musulunci.

Ita dai kotun ta yanke hukuncin ne wanda zai kama har na shekaru 22 abin ya yi kasa har zuwa shekaru 7 a gidan kaso a kansu baki baki daya.

3338779

Abubuwan Da Ya Shafa: ethiopia
captcha