IQNA

Ana Nuna Kin Amincewa Da Hukunta Wasu Musulmin Ethiopia

23:53 - August 05, 2015
Lambar Labari: 3339495
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin mabiya addinin muslunci a kasar Ethiopia sun nuna rashin gamsuwa da hukuncin da wata kotu ta yanke kan wasu musulmi bisa zarginsu da alaka da ta’addanci.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Reauters cewa, an samu wasu daga cikin mabiya addinin muslunci a kasar Ethiopia sun nuna rashin gamsuwa da hukuncin da wata kotu ta yanke kan wasu musulmi bisa zarginsu da dangantaka da wasu kungiyoyin ta’addanci.

wannan kotu ta yanke hukuncin ne a kan musulmi su 18 da suka hada har da wani malami da kuma wamni dan jarida, wadanda suka fada tarkon da aka dana musu kamar dai yadda ake zargin cewa an shirya hakan ne domin cin zarafinsu.

Ana danganta wannan hukunci da yadda wasu daga cikin musulmin suka nuna rashin amincewarsu da wannan hukunci sun ce, an dauki wannan mataki ne saboda wadannan mutane sun zargi gwamnatin Ethiopia da saka baki a cikin harkokin addini.

Mahkuntan kasar suna danganta wata kungiya mai suna Ahbash da musulmin kasar, da ta ce suna son su mayar da kasar ta musulunci baki daya, alhali wannan kasa ta mabiya addinin kirista ce.

A cikin shekara ta 2007 ana cewa adadin musulmin kasar 34 ne, amma kuma daga bisani wasu daga cikin musulmin suna cewa a halin yanzu adadin mabiya addinin muslunci a fadin kasar ya kai mutane kasha 50 cikin dari na al’ummar kasar baki daya.

3339162

Abubuwan Da Ya Shafa: ethiopia
captcha