Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na IBTimes ya watsa rahoton cewa, wasu gungun ‘yan bindiga sun kai hari kan otel din byblos da ke garin Sevare a tsakiyar kasar Mali a yau Juma’a da nufin sace baki ‘yan kasashen waje lamarin da ya janyo hasarar rayukan mutane akalla biyar ciki har da na sojojin Mali biyu tare da jikkatan wasu adadin jama’a na daban.
Majiyar rundunar sojin Mali ta sanar da cewar jami’an tsaron kasar sun yi kawanya wa otel din kuma daga cikin mutane biyar da suka rasa rayukansu har da daya daga cikin masu satar mutanen sakamakon ganin jigidar bama-bamai a jikinsa.
A cikin otel din na byblos akwai baki ‘yan kasashen waje biyar, uku daga cikinsu ‘yan kasar Afrika ta Kudu, sannan dan kasar faransa guda da kuma dan kasar gabacin turai guda daya.
Jami’an tsaron Mali sun samu nasarar ceto mutane 7 daga cikin mutanan da aka yi garkuwa da su a Otel din Byblos dake birnin Severe.
Dakarun Majalisar dinkin duniya (MINUSMA) sun Allawadai da harin tare da bayyana shi da cewa na ta’addanci ne da ke nufin kara dagula lamurra a kasar.
Kungiyar Ansaruddin kungiya ce mai tsatsauran ra’ayi na kafirta musulmi kamar dai sauran kungiyoyin yan ta’adda masu dauke da irin wannan mummunar akida.
3339982