IQNA

Wani Masallaci A Arewacin London Na Taimakon Marassa Galihun Birtaniya

19:35 - August 11, 2015
Lambar Labari: 3341290
Bangaren kasa da kasa, babban masallacin arewacin birnin London na gabatar da ayyuakn taimako ga mutane marassa galihu na kasar da hakan ya hada da abinci da kuma wasu daga cikin kayan bukatar rayuwa.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Aljazeera cewa, Muhamamd Ali mai kula da harkokin masallacin ya bayyana cewa suna gudanar da ayyukan nasu ne da nfin kara fito da matsayin addinin muslunci danagne da ayyukan jin kai.

Wannan babban masallacin arewacin birnin London na gabatar da ayyukan taimako ga mutane marassa galihu na kasar, kamar yadda kuma suke wayar da kan jama’a, dsaga cikin abubuwamn suke bayarwa akwai abinci da kuma wasu daga cikin kayan bukatar rayuwa na yau da kullum.

Ya ci gaba da cewa wannan shiri yana daga cikin abubuwan da wannan masallaci yake gudanarwa, kuma taimakon ya hada da musulmi da wadanda ba musulmi ba, kuma hakan ana gudanar da shi fiye da shekaru 10 da suka gabata.

Da dama daga cikin marassa galihu suna kai ziyara  awannan masallaci domin samun taimako.

Yanzu haka dai akwai musulmi da yawansu ya kai miliyan 3 a kasar ta Birtaniya baki daya.

Bincike ya tabbatar da cewa musulmin kasar Birtaniya sun fi kula da junansu da kuma sauran al’mmo,I fiye da sauran mutanen kasar wadanda ba muslmi ba.

3340782

Abubuwan Da Ya Shafa: lebanon
captcha