Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na (radioalgerie) cewa an fara gudanar da wani zaman taro mai taken tafarkin muslunci da zaman lafiya karkashin malaman Darikar Tijjaniyah a yankin Ain Madhi a gundumar Al-agwat a kasar Algeriya da nufin kara wayar da kan musumi akan koyarwar muslunci a dukkanin bangarori.
Wanann taro yana samun halartar masana da malaman addinin muslunci da kuma malaman jami’oi daga sassa na kasar, kamar yadda kuma ake gabatar da karatun kur’ani mai tsarki wanda dalibai kimanin 220 da suka samu horo suke gabatarwa a wurin.
Haka nan kuma ana gabatar da bayanai da makaloli a gaban mahalarta taron, wanda ke nufin kara fito da matsayin muslunci dangane da bayyanar sabuwar akidar kafirta musulmi, wadda tafi karfi a cikin kasashen larabawa a halin yanzu.
Kasar dai tana daga cikin kasashen da suke fuskantar hadarin wannanan akida wadda ta samu asali daga koyarwar akidar wahabiyanci da ke kafirta duk wani musulmi da baya dake da wanann akida ko kuma yake bin masu dauke da ita, duk kuwa da cewa wannan sabon lamari ne a kasar.
Jama’a a kasar Algeriya wadanda mafi yawansu suna bin tafarkin Darikar Tijjaniya ne, sna samun horon karatun kur’ani da kuma sauran ilmomi a duk lokacin da ake gudanar da taruka na kasa baki daya irin wadannan, tare da samun ganin malamai daga sassa na kasar.
A karshen karni na 17 na hijira miladiyya ne dai aka samu Darikar Tijjania a karkashin Abul Abbas Sheikh Ahmad Tijjani dan kasar Algeriya.
Darikar Tijjaniya dai day ace daga cikin hanyoyi na sufanci da ke da mabiya masu yawa a kasar Algeriya da kuma kasar Senegal.
3341804