IQNA

An Fara Wani Shiri Na Mara Baya Ga Mahaifa Mata Musulmi A Makarantun Faransa

20:14 - August 14, 2015
Lambar Labari: 3342982
Bangaren kasa da kasa, an fara aiwatar da wani shiri na mara baya ga itaye mata da suke fuskantar matsaloli a makarantun kasar Faransa domin sanun yancinsu kamar sauran ‘yan kasa.


Kamfanin dillancin labara Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na aynar gizo na National cewa, Safiyyah ita ce ta kirkiro da wannan kamfe wanda zai taimaka ma iyaye mata muusulmia  kasar ta Faransa domin su samun ciakken yancinsu.

Yankin Monpley na kasar Faransa na yawan iyalai musulmi da suka kai kimanin dubu 5, kuma suna fuskantar matsaloli na nuna musu banbanci da wariya saboda addininsu, wanda hakan kuma ya yi hannun riga da dokokin kasar da ma na kungiyar tarayyar turai.

A kan wannan shiri ya zama wata hanya mafi sauki domin bayyana wa duniya halin da suke cikia  yanin, da kuma yadda aka mayar da saniyar ware a cikin lamurra da kuma nuna musu banbanci da tsangwamna babu gaira babu sabat.

Daga cikin hanyoyin da suke amfani da su wajen bayyana wa duniya halin da suke cikia kwai hanyoyi na saa zumunta na facebook da sauransu, wanda hakan kuma yana yin tasiri matuka inda a halin yanzu ala tilas mahukunta sun fara mayar da hankali kan lamarin.

Kasar Faransa dai ita ce kasar da tafi yawan musulmi a nahiyar turai baki daya, kuma a halin yanzu adadin muslmin kasar yah aura miliyan 6 wanda hakan ya sanya su suka zama a matsayi na biyu a kasar bayan mabiya addinin kirista wadanda su ne suka fi yawa a kasar.

3341689

Abubuwan Da Ya Shafa: faransa
captcha