IQNA

Muqtada Sadr Ya Jinjina Wa Sheikul Azhar Kan Hana Kafirta ‘Yan shi’a

23:44 - August 15, 2015
Lambar Labari: 3344505
Bangaren kasa da kasa, Moqtada Sadr yay aba wa babban malamin cibiyar Azahar dangane da matsayinsa na kin amincewa da kafirta mabiya mazhabar shi’a da wasu ke yi tare da bayyana cewa a shirye yake ya yi salla a bayan shi’a.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Saumariyyah News cewa, Moqtada Sadr ya jinjina wa  Sheikhul Azhar Kan matsayinsa na kin amincewa da kafirta mabiya mazhabar shi’a, bayan haka kuma ya ce a shirye yake ya yi salla a bayan shi’a a birnin Najaf, y ace matsayin Ahmad Tayyib abin yabawa ne matuka.

Moqtada Sadr ya ce ko shakka babu irin wannan matsaya da babban malamin ciyar ta Azahar ya dauka abin yabawa ne, kuma hakan ya kara tabbatar da cewa akwai malami masu adalci da bayyana gaskiya komai dacinta a tsakanin malamai, wanda hakan zai kara kawo hadin kai tsakanin musulmi baki daya.

A kwanakin baya ne malamin an Azhar ya ce babu dsalili na kafirta shi’a a cikin kur’ani da sunnar manzo, kuma idan ya yi tafiya zuwa Iraki zai kai ziyara zuwa birnin najaf domin haduwa da manyan malaman shi’a, saboda babu wani dalili na kafirta mabiya mazhabar shi’a a cikin kur’ani mai tsarki da sunnar manzon Allah da wasu tashoshi suke yi a kullum domin haifar da fitini tsakanin al’ummar musulmi.

Idan za a iya tunawa sheikh Ahmad Tayyib ya ce aiki na farko da ke gaban cibiyar Azhar a halin yanzu shi ne hankoron ganin an samu hadin kai tsakanin dukkanin al’ummar musulmi, wanda hakan ya hada dukkanin bangarori na musulmi baki daya.

Haka nan kuma ya ce kwanaki baya ya gana da wata tawaga daga kasariIraki, wadda ta kunshi dkkanin bangarori na musulmin kasar, saboda haka shi ma nan ba da jimawa ba zai tafiya zuwa kasar Iraki kuma zai gana da dkkanin bangarori.

3343243

Abubuwan Da Ya Shafa: iraki
captcha