Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na KSAT wani jami’in Amurka a Texas ya bayayna cewa ya zama wajibi a kansu su dauki matakan murkushe musulmi da hakan ya hada da yin amfani da makaman nukiliya.
A cikin shekaru 1945 gwamnatin Amurka ta yi amfani da makaman nukiliya na kare dangi a kan garuruwa Heroshima da Nagazaki na kasart Japan, inda ta kashe mutane dubu 210 daga faren hula na wadannan garuruwa.
Wannan bayani nasa dai ya zoa shafinsa na yanar gizo, duk kuwa da cewa da dama daga cikin yan siyasa na kasar da ma kungiyoyin kare hakkin bil adama sun bayyana takaici matuka dangane wanann furuci wanda ba shi da ma’auni na hankali.
Jami’ai da dama a cikin ta Texas sun yi kakakusar suka tare da yin kira da a tuhumce shi da kokarin haifar da tashin hankali a cikin duniya, duk kuwa da cewa akwai wasu masu tsatsaruran ra’ayi da suke goyon bayan abin da ya fada .
Ana ci gaba da sanya ido domin ganin irin matakan da mahukunta a jahar ta Tezas za su dauka domin ladabtar da wannan dan majalisar mai hankoron kawo tashin hankali a cikin kasar ta Amurka ta hanyar yada kalaman kin jinni ga wani jinsi da addini.
3345949