IQNA

An Bukaci Da A Tsaurara Matakan Tsaro A Masallatan Kasar Amurka

18:15 - August 20, 2015
Lambar Labari: 3349406
Bangaren kasa da kasa, an bukaci da a dauki matakan tsaurara matakan tsaro a masallatan kasar Amurka sakamakon bayanan da aka samu daga wasu masu adawa da musulmi da ke neman kai hari kansu.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sporting cewa, babban cibiyar mabiya addinin muslunci a kasar Amurka (CAIR) ta bukaci da a dauki matakan tsaurara matakan tsaro a masallatan kasar Amurka da ke jahohin daban-daban, bayan samun labarin barazanar kai musu hari.

A ranar 18 ga watan Agustan nan ne wannan cibiya ta aike da sako zuwa ga babban hukumar yan sanda mai gudanar da bincike kan ayyuka na laifuka a kasar ta Amurka wato (FBI), da nufdin sanar da hukumar halin da ake ciki na barazanar da ake yi wa musulmi.

Wasu daga cikin kungiyoyin masu tsatsauran ra’ayi sun yi barazanar cewa za s kai hare-hare kan mabiya  addinin muslunci a cikin masallatai da suka fadin kasar ta Amurka, bayan da suke danganta musulmi da kuma addinin muslunci da ayyukan ta’addanci.

A kwanakin baya ne wasu daga cikin yan majalisar dokokin kasar Amurka suka gabatar da shawar cewa ya kamata  aware kimanin kudi dala miliyan 40 domin yaki da wsu masu tsatsauran ra’ayi a kasar da suke takura ma musulmi da ma wasu wadanda suke marassa rinjaye a kasar.

3349210

Abubuwan Da Ya Shafa: amurka
captcha