Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Shafaqana cewa, yan ta’addan Daesh sun kame wasu muaten 6 dukkaninsu fararen hula agarin Karkuk na kasar Iraki inda suka yi musu kisan gilla a bainar jama’a, bisa hujjar cewa sun bar muslunci sun karbi shi’a, inda suka tsire su a kan turaku.
Wani shafi mai alaka da yan ta’addan ya nuna hotunan mutanen shida a lokacin da aka daure su tare da karanta musu bayani daga daya daga cikin ‘yan ta’adda da ya rufe fuskarsa a kan titi, kafin daga bisani a dauke su zuwa wani dandali inda aka tsire su baki daya.
Wannan mummun aiki da yan ta’addan suke aikatawa bas hi na farko, kusan dais hi ne abin da suke yi a kowace rana adukaknin garuruwan da suka kwace iko da su a cikin Iraki, kamar yadda kuma suke danganta hakan da fatawar da suke samu daga littafan magabansu da suka rubuta na kafirta al’mmar musulmi da halasta jininsu.
3349483