IQNA

23:56 - August 26, 2015
Lambar Labari: 3353043
Bangaren kasa da kasa, majalisar dinkin duniya ta yi gargadi dangane da kashe kanann yara da masatar Saudiyya ke ba ji ba gani a kasart Yemen.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Press Tv cewa,

hukumar kula da mata da yara ta majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa yara kimani dari hudu ne aka kashe tun lokacinda kasar.Laila Zaruki wakiliyar hukumar ce ta sanad da hakan inda ta ce saudia da kawayenta suka fara kai farmaki kan kasar Yemen a ranar ashiorin da biyar  ga maris na wannan shekara.Julien Harneis, wakilin hukumar a kasar yemen ne ya bayyana haka a wani rahoton da ya fitar dangane da halin da yara kanana suke a cikin kasar ta Yemen.Jami’ar ta kara da cewa a hare-haren an wuce godna da iri  a yau sun kashe mutane 65 daga cikinsu har da kanan yara 17,bBanda haka wasu yara da dama suna cikin hatsarin kamuwa da cutar tamowa ko yunwa nan gaba a cikin wannan shekara.Rahoton ya kara da cewa hare haren kasar saudia da kawayenta sun rusa kashi casein na makarantu a kasar, sannan an lalata wasu, tare da kashe yara 398 da kuma jikkata wasu 605 ya zuwa yanzu, makarantun an rusa 114 an lalata 315.Manufar kasar saudia da kawayenta na farwa kasar yemen  da yaki dai ita ce maida tsohon shugaban kasar , haka nan k ungiyar kare hakkin bil adama ta duniya ta yi Allawadai da kakkausar murya dangane da hare-haren da jiragen yakin Saudiyyah suka kai kan gabar ruwa ta garin Hudaidah na kasar Yemen.A cikin bayanin da kungiyar ta fitar a jiya ta bayyana cewa, hare-haren da jiragen Saudiyya suka kai a cikin wannan mako a kan gabar ruwa ta Hudaidah tare da kashe fararen hula, hakan daidai yake da laifukan yaki, wadanda kotun manyan laifuka ta duniya kan shari’a a kansu.A kan haka hukumar ta bukaci majalisar dinkin duniya da ta gudanar da binciken gaggawa kan harin na Saudiyyah a Hudaidah tare da bayar da rahoto kan hakan.Tashar talabijin din ta bayar da rahoto a daren jiya Alhamis daga garin Ta’iz na kasar Yemen cewa, farare hula da suka hada da mata da kananan yara ne suka rasa rayukansu, sakamakon wasu hare-hare da jiragen yakin Saudiyya suka kaddamar a kan gidajen jama’a a garin na Ta’iz a daren na jiya.3351759

Abubuwan Da Ya Shafa: Yemen
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: