IQNA

Jordan Ta Yi Allawadai Da Rufe Kofofin Masallacin Aqsa Da Isra’ila Ta Yi

22:40 - August 27, 2015
Lambar Labari: 3353178
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin Jordan ta yi Allawadai da kakkausar murya dangane da rufe kofofin masallacin Aqsa da haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gzo na Xin Huwa cewa, kakakin gwamnatin Jordan Muhammad Mu’mini ya bayyana cewa suna yin Allawadai dangane da rufe kofofin masallacin Aqsa da haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi da nufin tsokanar musulmi.

Ita ma a nata bangaren kungiyar hadin kan kasashen larabawa ta yi Allawadai da ke alfarmar wurare masu tsarki da yahudawan sahyuniya suke yi a birnin Quds da ma sauran yankunan Palastinu, gami da cin zarafin palastinawa marassa kariya.



Babban jami’in mai kula da harkokin Palastinu a cikin kungiyar hadin kan kasashen larabawa ne  ya sanar da hakan a jiya a babban ofishin kungiyar da ke birnin Alkahira na kasar Masar, inda ya ce kungiyar tana nuna takaicinta matuka dangane da yadda yahudawan sahyuniya suke ta tsananta ayyuknsu na cin zarafin Palastinawa da yi musu kisan gilla, da kuma keta alfarmar wurare masu tsarki da ke wurin.



Haka na ya ce kungiyar za ta ci gaba da bin dukkanin hanyoyi da suka dace domin kalubalantar gwamnatin yahudawan Isra’ila da nufin taka mata birki kan wannan ta’asa ta yahudawan sahyuniya.



Tun a cikin shekara ta 1994 ne dai gwamnatin Jordan take sanya ido kan muhimamn wurare na mabiya addinin musulunci da kuma kirista a cikin birnin Quds mai alfarma.



3353120

Abubuwan Da Ya Shafa: quds
captcha