IQNA

Hidima Ga Al’ummar Musulmi Shi Ne Babban sakon Cibiyar Azhar

22:12 - August 28, 2015
Lambar Labari: 3353316
Bangaren kasa da kasa, Ahmad Tayyib ya bayyana cewa bababn sakon cibiyar Azahar ga dukkanin duniyar musulmi shi ne hidima ga addinin muslunci da musulmi baki daya.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bawwabah News cewa, Ahmad Tayyib Sheikhul Azhar a lokacin ganawarsa da Sayyid Mustafa Auzjan na kasar Turkiya ya bayyana cewa, hidima ga addinin muslunci da musulmi baki daya shi ne sakon Azhar.

Ya ci gaba da cewa a kowane lokaci suna kokarin ganin sun isar da sakon addinbin muslunci a dkknin bangarori na duniyar musulmi tare da yada ilimi, wamnda kuma shi ne babban aikin wannan cibiya ta sunna a duniya ta amfanar da mabiya wannan addini.

Dangane da irin alakar da ke tsakanin Azhar da kum aal’ummar Turkiya, ya bayyana cewa hakika an dauki tsawon lokaci bangarorin biyu suna da kyakyawar alaka ta addini da kuma ilimi, inda cibiyar takan aike da malamai domin koyar da Trkawa.

Ahmad Tayyib yace akwai masu bincike Turkawa da sukan ziyarci Azahar a kowane lokaci domin gudanar da bincike mai zurfi a dukkanin bangarori na ilimi.

Sayyid Mustafa Auzjan a nasa bangaren ya bayyana cewa, dangataka da ke tsakanin Turkawa da kuma cibiyar Azahar dangataka ce ta tarihi, wadda take da alaka da addini, kasantuwar Azhar ita ce bababr cibiyar muslunci a mahangar sunna a duniya baki daya.

3353258

Abubuwan Da Ya Shafa: azhar
captcha