IQNA

Wani Malamin majami’ar kirista Ya Muslunta A Kasar Rwanda

22:57 - August 31, 2015
Lambar Labari: 3355700
Bangaren kasa da kasa, wani malamin wata majami’ar mabiya addinin kirista a kasar Rwanda ya karbi addinin muslunci tare da dukkanin wadanda suke bauta a cikin majami’ar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na leral.net cewa, wannan malamin majami’ar kiristoci ya musulunta ne tare da dukaknin iyalansa da kuma wadanda suke tare da shi baki daya.

A ranar Taata 25 ga watan Agusta mutumin tare da mutanensa sun taru a wannan majami’a, maimakon yin ibadunsu na addinin kirista kamar yadda suka saba, sai suka shelanta karbar addinin muslunci baki daya.

Wannan malamin majami’ar kiristoci ya muslunta ne bayan tattaunawa tare da wani malamin addinin muslunci dan asalin kasar, wanda ya gamsar da shi dangane da addinin muslunci cewa shi ne gaskiya, kuma an mayar da majami’ar zuwa masallaci.

Kasar Rwanda tana daya daga cikin kasashen masu kyauwun dabi’a a tsakanin koramun nahiyar Afirka, kuma babban birnin kasarshi ne Kigali a halin yanzu.

3354439

Abubuwan Da Ya Shafa: Rwanda
captcha