IQNA

An Shirya Taron Bayar Da Horo Kan Aikin Hajji A Senegal

23:19 - September 01, 2015
Lambar Labari: 3357104
Bangaren kasa da kasa, an shirya taron bayar da horo kan aikin hajji karkashin jagorancin ofishin yada al’adu na Iran a kasar Senegal.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na hulda da jama’a a cibiyar yada al’adun muslunci cewa, an gudanar da wannan taron bayar da horo ne mai taken (Hajji) kakashin himmar ofishin yada al’adu na Iran a Senegal, tare da halartar mutane 80 maza da mata dkkaninsu maniyyata.

Sayyid Hassan Esmati shugaban ofsihin yada al’adu na kasar Iran a Senegal ya yi ishara a lokacin bayar da horo da cewa; shi wannan aiki yana tabbatar da hadin kai na muslunci da ke akwai tsakanin musulmi da kuma bayyana Imani da ubangiji.





Ya kara da cewa shi aikin hajji wani horo ne na musamman da ke koyar da mutun biyayya ga Allah, gudun duniya, tuna mutuwa da hadin kan musulmi, a wannan shekara kimanin mutane dubu 10 ne daga kasar Senegal suke da niyyar safke farali.





Abin tuni a nan shi ne wannan horo ya koyar da abin da ake yi kafin tafiya haji, na akida da akhlaq na muslunci da kuma sanin muhimman lamurra kan tarihi, da kuma wurare da ke cikin Makka da Madina.

3355765

Abubuwan Da Ya Shafa: senegal
captcha