IQNA

An Yi Allawadai Da Mamaye Makabartar Musulmi Ta Babu Rahma Da Sahyuniyawa Suka Yi A Quds

22:48 - September 02, 2015
Lambar Labari: 3357557
Bangaren kasa da kasa, kwamitin musulmi da kiristoci ya yi kan mamaye wane bangare na babbar makabartar musulmi ta Babu Rahma da ke kusa da masallacin Quds mai alfarma da yahudawa suka yi.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga Ina cewa, a yau ne  jami’an tsaron yahudawan sahyuniya sun mamaye wane bangare na babbar makabartar musulmi ta Babu Rahma da ke kusa da masallacin Quds mai alfarma.

A yau ne da jijifin safiya jami’an tsaron yahudawan sahyuniya suka kaddamar da farmaki kan wanann wuri mai matsayi a wajen musulmi inda suka mamaye wani bangare na makabartar a wani mataki na tsokanar mabiya addinin muslunci kamar dai yadda suka saba.

Babbar manufar yahudawan sahyuniya ta yin hakan dai ita ce kokarin mamaye wurare mallakin musumi musamman ma wurare da mabiya addinai na muslunci da kiristanci suke girmamawa, domin mayar da su karkashin su ko kuma rusa su kowa ya rasa.

A kan haka ne kwamitin da ke kula lamurran mabiya adinan muslunci da kiristanci a birnin na Quds ya fitar da bayani a yau, inda ya yi Allawadai da akkakusar murya kan wannan mummunai aiki na tsokana, tare da yin kira ga gwamnatin yahudawan da ta kiyaye hakkokin addinai.

Wannan kwamitin ya tababtar a cikin bayanin da ya fitar cewa makamabartar Babu Rahma ta musulmi ce tantagarya, kuma keta alfarmar wannan wuri daidai yake da keta alfarmar wurare masu tsarki na mabiya addinin kiristanci.

Hana Isa shugaban kwamitin musulmi da kiristoci na birnin Quds ya bayyana cewa, wanann bas hi ne karon farko da yahudawan sahyuniya suka aikata irin wannan tabargaza ba, domin kuwa a lokutan baya sun mamaye kimanin mita 1800 daga cikin wannan makamabrta ta musulmi.

Wannan makabrat dai tana daya daga manyan makabartu na tarihin addinin muslunci, inda aka rufe wasu daga waliyayyi da kuma sahabban manzo a cikinta.

3357450

Abubuwan Da Ya Shafa: quds
captcha