IQNA

Hizbullah Ta Yi Suka Dangane Da Yadda Kasashen Duniya Suka Yi Kan Makomar Imam Musa Sadr

22:50 - September 02, 2015
Lambar Labari: 3357558
Bangaren kasa da kasa, kungiyar gwagwarmayar muslunci ta Hizbullah Lebanon ta yi kakkausar suka dangane da yadda kasashen duniya da kuma wasu daga cikin kasashen yankin suka gum da bakunansu kan makomar Imam Musa Sadr.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Almanar cewa, kungiyar Hizbullah ta fitar da bayani dangane da tunawa da ranar sace Imam Musa Sadr da aka gudanar da tarukanta a jiya.

A cikin baynin na kungiyar ya zo cewa, Imam Musa Sadr shi ne mutumin da ya raya gwagwarmayar neman hakki a cikin zukatan al’ummomin kudancin kasar Lebanon musamman ma matasa daga cikinsu, inda hakan yay i sanadiyyar nasarasu a shekara ta 2000 da kuma shekara ta 2006.

Bayanin na kungiyar Hizbullah y ace duk da wucewar shekaru 37 da sace Imam Musa Sadr, amma har yanzu yana nan a cikin zukatan jama’a, kuma abin da ya yi yana  araye kuma yana ci gaba da kara bunkasa kamar yadda dukaknin duniya ta sheda hakan.

Hizbullah ta ce babu wani dalili da zai iya wanke wannan babban laifi na sace Imam Musadr a tarihin wanann al’umma, kamar yadda kuma sace ba zai iya tsayar da abin da ya kafa ba ko kuma hakan ya sanya masu bin tafarkinsa su yi sanyi da abin da suke yi.

Daga karshe bayananin y ace al’ummar Lebanon za su ci gaba da kasancewa kan tafarkinsa da ya dora sun a neman izza da karama, kuma zai ci gaba da kasancewa tare da su a cikin zukatansu ko da kuwa bay a a cikinsu a gangar jiki, kuma Isra’ila za ta ci gaba da kwasar kaskanci daga masu bin tafarkinsa.

3355946

Abubuwan Da Ya Shafa: Hezbollah
captcha