Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bawwaba Alkahira cewa, a jiya an fara gudanar da sharar fage na gasar hardar kur’ani mai tsarki karo na 25 na cibiyar Sarki Qabus na kasar Oman.
Bayanin ya ce wannan gasa za ta gudana a matakai na hardar kur’ani, da ya hada da dukkanin kur’ani da kuma 24 sai kuma 18 da kuma 12, haka nan kuma wadanda za su gudanar da gasar shekarunsu sun kama daga 15 a bin ya yi sama kamar dai yadda cibiyar ta sanar.
An fara ne tare da halartar alkalan gasar a masallacin Bushar da ke cikin gndumar Maskat babban birnin kasar, wanda kuma wannan mataki na sharer fage, bayan kammala tantancewa za a sanar da wadanda suka cancanci wucewa zuwa gaba.
Mahardata kimanin 106 ne suke halartar gasar ta sharer fage a wannan yanki, amma bayan kammalawa za a gudanar da babbar gasar tare da halartar sauran wadanda suka cancan wucewa daga suran yankuna na kasar baki daya, da za su kai 1558 maza da mata.
Babbar manufar gudanar da wannan gasa dai ita ce karfafa matasa wajen mayar da hankali ga lamurra da suka shafi kur’ani mai tsarki a kasar, da kuma sauran bangarori na addinin muslunci kama daga karatu da harda da kuma sanin ilmin kaidojin karatun, da sauran hadisai da hukuncin addini na sha’aria ta musulunci.
3357300