IQNA

Nuna Hotunan Yaro Dan Syria Da Ya Nutse Ya Tayar Da Hankalin Bil Adama

23:51 - September 06, 2015
Lambar Labari: 3358800
Bangaren kasa da kasa, nuna hotunan yaron nan dan kasar Syria Ailan Kurdi da ya nutse a cikin ruwa ya tayar da hankulan bil a dama a duniya a baki daya.


Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na ayanr gizo na kungiyar kasashen musulmi OIC cewa, kungiyar ta nuna kaduwa dangane da yanayin da ‘yan gudun hijira na Syria suke ciki musamman ma nutsewar yaro akrami a cikin ruwa.

A nasa bangaren shugaban kasar rash ya dora alhakin kwarar ‘yan gudun hijira daga kasar Syria zuwa nahiyar turai a kan kasashen yammacin turan, sakamakon mummunar rawar da suka taka wajen kunna wutar rikicin kasar ta Syria.

Ya ce tun kafin wanann lokacin sun gargadi kasashen yammacin turai dangane da babban kuren da suka tafka wajen  mara baya kai tsaye ga ‘yan ta’adda a Syria domin cimma manufofinsu an siyasa kan gwamnatin kasar.

Abin da yake faruwa kuma yanzu na kwararar ‘yan gudun hijirar zuwa turai domin neman mafaka sakamako ne na haifar da ta’addanci da aka yi a cikin kasarsu wadda suke zaune lami lafiya a cikinta, suna gudu ne domin tsira daga ‘yan ta’adda ba suna gudu ba ne saboda shugaban kasar ba.

Ya kara da cewa, za su ci gaba da taimaka ma gwamnatin ta fuskar soji, domin ta kare kanta daga barazanar ta’addanci da kuma masu mara ma ‘yan ta’addan baya. Haka nan ya kara da cewa da sannu kasashen yammacin turai za su ci gaba da gane babban kuren da suka tafka a syria da ma wasu kasashen larabawa na gabas ta tsakiya.

3358568

Abubuwan Da Ya Shafa: oic
captcha