Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Lebanesefiles.com cewa, Hibullah ta fitar da bayani da cikinsa ta yi kakakusar suka da Allawadai da kisan kiyashi na dabbanci da Saudiyya da Amurka suke yi kan al’ummar kasar Yemen marassa kariya tare da yin shiru daga sauran kasashe.
Hare-haren wuce gona da irin kasar Saudiyya kan garin Ibb da ke kudancin kasar Yeman sun yi sanadiyyar shahadar mutane akalla sha biyu, tare da jikkata wasu hamsin da hudu na daban.
Majiyar tsaron Yamen ta sanar da cewa jiragen saman yakin Masarautar Saudiyya sun kai hare-haren wuce gona da iri da makamai masu linzami kan gidajen mutane a tsakiyar garin Yarim da ke lardin Ibb a jiya Litinin, inda suka yi sanadiyyar kashe mutane akalla sha biyu.
Har ila yau sun yi sanadiyyar rusa gida masu yawa lamarin da ya tilastawa jama’ar yankin barin muhallinsu. Mahukuntan Saudiyya da sauran kasashen Larabawa da suke goya musu baya a yaki kan kasar Yemen sun kara karfafa yawan sojojinsu tare da jibge tarin makaman yaki da nufin bullo da wani sabon salon murkushe al’ummar Yemen.
Kungiyar Hizbullah ta bayyana shiru da majalisar dinkin duniya ta yi tare da sauran kasashen duniya ya kara tabatar da cewa sun bayar da lasisin kashe al’ummar kasar Yemen da rusa musu kasa, tamka sub a yan adam ba ne da ke rayuwa abayan kasa kamar kowane mutum.
3360703