IQNA

Wajibi Ne A Kafa Kawance Domin Yaki Da ‘Yan Ta’addan Daesh

23:41 - September 16, 2015
Lambar Labari: 3364400
Bangaren kasa da kasa, Nikolai Moladnuf wakilin majlaisar dinkin duniya kan harkokin yankin gabas ta tsakiya ya bayyana cewa dole ne akfa kwance domin yaki da daesh.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na novinite.com cewa babban wakilin majlisar dinkin duniya kan yankin gabas ta tsakiya Nikolai Moladnof ya bayyana cewa, abin da kasashen turai suke na kai hari kan yan ta’adda Daesh ba zai taba wadatarwa ba.

Wasu na ganain cewa kasashen larabawa za su iya taka rawa wajen shawo kan wanann lamari to sai dai wasu masu bin diddigin lamarin siyasar kasashen larabawa na saka alamar tambaya kan yadda kasashen larabawa za su yi yaki da ta’addanci a wasu kasashen.

Musamman ganin cewa wasu daga cikin manyan kasashen larabawan ne masu tasiri suke da hannu kai tsaye wajen haifar da rikicin kasar ta lib, domin kifar da marigayi da suke takon saka da shi, kamar yadda kuma suka ci gaba da daukar nauyin kungiyoyin ‘yan bindiga daban-daban da suka rarraba kasar a halin yanzu.

Wanda kuma shi ne abin da gwamnatocin kasashen larabawan suke yi a halin yanzu a kan wasu kasashen ‘yan uwansu, wanda hakan ya sanya  masanan ke ganin cewa da wuya a samu hadin kai a tsakanin larabawa da zai iya kawo karshen kungiyoyin ta’addanci a cikin kasashensu, domin kuwa wasu daga cikin manyan kasashen larabawan suna amfani da kungiyoyin ‘yan ta’addan ne a matsayinwani babban makami na cimma manufofinsu na siyasa.

3363182

Abubuwan Da Ya Shafa: daesh
captcha