IQNA

Taro Kan Yadda Ake Koyon Harda Da Kuma Karatun Kur’ani A Kasar Libya

23:08 - September 19, 2015
Lambar Labari: 3365121
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani zaman taro kan yadda ake koyar da hardar kur’ani mai tsarki da kuma karatunsa a kwalejin ilimi ta garin Darj da ke yammacin kasar Libya.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tafsir.net cewa, a jiya ne aka gudanar da wani zaman taro kan yadda ake koyar da hardar kur’ani mai tsarki da kuma karatunsa da nufin kara matsayin masu karatu da harda  akasar.



Bayanin ya ci gaba da cewa an samu halartar malamai da masana daga sassa na yammacin kasar da suka gabatar da jawabai ga dalibai da suke karatu a wannan fage, da nufin kara karfafa gwiwarsu.



Daga cikin malaman akwai Sheikh Muhammad bin Naser Alghadamsi, Muhamamd Timsah, kamil Alma’ali, Abdulkadir Muhammad Dau, Abdlrazaq Hisn duk sun halarci wurin taron.



Haka nan kuma an girmama da dama daga cikin dalibai da suke nuna kwazo matuka wajen lamarin da ya shafi harkar karatu da hardar kur’ani mai tsarki a kasar, da sukan halarci tarukan wakiltarta a waje da ciki.



Daga karshen an gabatr da laccoci na jan hankali ga matasa da su mayar da hankali matuka kan lamarin kur’ani mai tsarki, domin kuwa hakan shi ne babban abin da zai ba su damar zama masu amfanar da kasar a gaba.



3364977

Abubuwan Da Ya Shafa: libya
captcha