IQNA

Tushen Musifar Da Ake Fama Da Ita A Halin yanzu Ta Samo Asali Ne Daga Rarrabar Kai Ta addini

22:07 - September 22, 2015
Lambar Labari: 3366439
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kasashen msuulmi ta ce babbar musifar da ake fama da ita ahalin yanzu ta samo asali ne daga rarrabar kawunan musulmi da ake fama da ita a halin yanzu.


Kamfanin dillancin labarn Iqna ya hbarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, Iyad Amin Madani babban sakataren kungiyar kasashen musulmi ya bayyana cewa musifar da musulmi ke fama da ita a halin yanzu tafi muni a kan kowane lokaci.

Inda ya ce babbar musifar da ake fama da ita a yanz ta ta’addanci da kafirta musulmi samo asali ne daga rarrabar kawunan musulmi bisa ta’assubanci na bangaranci marassa tushe wanda ba shi ne asali ba.

Ya ci gaba da cewa dole ne a karfafa batun sulh da fahimtar jna da ajiye duk wani banbanbci na addini domin hada kai a fuskanci babbar matsalar da take addabar muslmi a yanzu, ita ce ta’addanci da sunan addini.

Tun a cikin shekarun da suka gabata ne aka fara batn sulhu da kusanto da fahimtar juna a tsakanin msulmi, amma wasu dag cikin kasashen da suke da hannu wajen ganin an rarraba kan msuulmin suka ki amincewa da hakan.

Wata bababr matsalar da ake fama da ita wadda it ace tushen dukaknin matsaloli ita ce yadda kasashen da su ne suke da karfin fada  aji a kungiyar kasashen msuulmi suka zama su ne kan gaba wajen haddasa dukkanin matsalolin da musulmi suke fama da su yanzu a duniya.

An fara wannan batu na sulhu ne tuna  cikin shekarun da suka gabata a matsayin ranar 21 ga Satmba ta zama ranar sulh a tsakanin musulmi dama sauran mutane baki daya.

Ta yadda hakan zai kara karfafa ruhin yan adamtaka a tsakanin dukkanin bil adama, kmar dai yadda aka aka ajiye tun a cikin sheklara ta 1982 kan gudanar da irin wannanzama, wanda har yanzu bai yi nasara ba.

3366256

Abubuwan Da Ya Shafa: oic
captcha