Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Reauters cewa, a lokacin da yake gabatar da wani jawabi jiya a gaban majami’ar birnin New York na kasar Amurka, jagoran na mabiya addinin kirsita ya damuwarsa matuka dangane da abin da ya faru Makka a jiya.
Ya ce ko shakkbabu abin da ya faru jiya ga mahajjata abin bakin ciki ne matuka, kuma ya ce ci gaba da sanya wadanda suka rasu addu’a da kuma wadanda suka samu raunuka ubangiji ya ba su lafiya.
Kasashe da dama a duniya sun aike da sakon taya musulmi alhinin abin da ya faru na mutuwar alhazai a Mina a jiya, da suka hada da Turkiya, Birtaniya, Amurka, Faransa da kuma Indonesia kana bin da ya far na mutuwar mahajjata musulmi a Mina da suka hada da Iraniyawa 131 dukkaninsu masu aikin hajji.
Wannan abin bakin ciki ya faru ne kasa da makonni biyu da faruwar wani lamarin na daban a cikin masallacin harami inda wani karfen daukar kaya ya fado ya kashe mutane fiye da 100, wasu kuma suka samu raunuka.
3367182