IQNA

Cibiyar Hubbaren Alawi Ta Ce A Shirye Ta Karbi Miliyoyin Masu Taron Ghadir

23:18 - September 30, 2015
Lambar Labari: 3375974
Bangaren kasa da kasa, cibiyar da ke kula da hubbaren Aalawi ta sanar da cewa a shirye take ta karbi miliyoyin masu ziyara a ranar Ghadir daga ko’ina cikin duniya.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na bangaren hulda da jama’a na hubbaren Alawi cewa, an fara kafa alluna na maraba da bakin idin Ghadir Khom a wannan wuri mai tsarki.

Bayanin y ace an kafa wadannan alluna da suke dauke da hadisan Imam Ali (AS) a koina da suke bayyana matsayin wannan wuri mai albarka, wanda aka n gudanar da taruka na tunawa da ranar Ghadir kamar yadda aka saba yi.

Wannan cibiyar ta hbbaren Imam ali (AS) ta kasance daya daga cikin manyan cibiyoyi da suke shiryya tarukan muslunci a kowace shekara a kan lamurra daban-daban da suka shafi iyalan gidan amnzon (AS)

Allunan da aka kafa a wannan wuri mai tsarki da albarka da suke dauke da kalaman Imam Ali (AS) suna bayani kan matsayin wannan bawan Allah da kuma shi’arsa da matsayinsu a wurin ubangiji, adadins ya kai 42 a wannan karo.

A kowace shekara miliyoyin mutane ne daga sassa na duniya daga cikin mabiya tafarkin iyalan gidan manzo (AS) da ke kan tafarkin shi’ar Imam Ali (AS) da suke zuwa ziyara da ayyukan ibada a wannan wuri mai tsarki.

3375754

Abubuwan Da Ya Shafa: iraki
captcha