Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al-alam cewa, Sheikh Naim Qasem a shafinsa na Facebook mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbllah ya bayyana cewa dora alhakin abin da ya faru a Mina kisan alhazai yana kan mahukuntan saudiyya tare da neman da su bari agudanar da bincike kan bin da ya faru da zai hada dukkanin bangarori na kasashen musulmi.
Shi ma wani likitan kasar Masar ya yi zargin cewa an fesawa mahajjata iska mai guba ce a Mina Kafar watsa labarun al-mudih, ta Saudiyya ta buga cewa; likitan wanda likita ne dan kasar masar, kuma jami’i na ma’aikatar kiwon lafiyar Saudiyya, ya rbutawa sarkin Saudiyya wasika da aciki ya yi zargin cewa an yi amfani da guba akan mahajjata.
Likitan ya ci gaba da cewa baya da ya bincika gawawwaki masu yawa da su ka fadi a Mina, sannan kuma da ganin wasu da su ka tsira, ya kai ga cimma matsaya cewar an yi amfani da iska mai guba., a can kasar Masar ma likitoci da dama sun bayyana cewa mutanen da su ka jkkata wadanda aka kai su asibiti, sun kamu da cutar manutuwa.
Dubban mahajjata ne dai da su ka fito daga kasashe daban-daban na duniya su ka rasa rayukansu, bayan toshe wata daga cikin hanyoyi da aka yi a wurin jifar shaidan, hukumomi a kasar Saudia sun tabbatar da mutuwar mutane fiye da dubu hudu a hatsarin ranar Alhamis da ta gabata a garin Mina, tashar television ta
Tashar talabijin mai watsa shirye shiryensa da harshen turanci ta nakalto mataimakin ministan lafiya na kasar saudia yana fadar haka a yau talata , alduwaila ya kara da cewa mutane dubu hudu da dari bakawai en aka tabbatar da mutuwarsu a cikin mahajjata a Mina a ranar al-hamis sannan tsananin zafi da kuma rashin iska ne suka kashe mafi yawansu.