IQNA

‘Yan Sanda Ba Su Damuwa Da Mutane / A Mina Kiyama Ce Aka Yi

23:20 - October 05, 2015
Lambar Labari: 3382030
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin alahazan kasar Masar sun bayyana abin da ya faru a Mina da cewa balai ne mai girma.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Shafaqna cewa, wasu daga cikin alahazan kasar Masar ad suka tsira daga abin da ya faru a aikin bana sun bayyana abin da cewa ya yi kama da tashin duniya.

Rashin kula da nuna halin ko-oho gami da rashin daukan matakan da suka dace; sune suka janyo hasarar rayukan mahajjatan bana a Mina.



Muhamamd Jazzar yana mai fayyace cewa, a mahangar Jamhuriyar Musulunci lallai akwai rina a kaba dangane da abin da ya faru a Mina, sakamakon haka ya zame dole a kan mahukuntan Saudiyya su yi aiki da hakkin da ya rataya a wuyarsu a karkashin dokokin kasa da kasa tare da fayyace wa duniya hakikanin abin da ya janyo faruwar wannan hatsari.



A nashi bangaren kakakin gwamnatin  ya yi furuci da cewa; Jamhuriyar Musulunci zata mika batun matsalar Mina zuwa gaban hukumomin kasa da kasa domin bin bahasin lamarin sakamakon matakin da mahukuntan Saudiyya suka dauka na neman wofantar da matsalar tare da rashin mutunta gwamnatocin kasashen da mahajjatansu suka rasa rayukansu.



Ya kara da cewa ba za su amincewa da batun neman bisine mahajjatan kasar a Saudiyyah ba, don haka dole ne a kan mahukuntan na Saudiyya su hanzarta mikawa kasar gawawwakin mahajjatanta tare da fayyace hakikanin musabbabin faruwar wannan hatsari mai tada hankali a filin Mina.



A gefe guda kuma ministan lafiya na kasar a halin yanzu haka yana ci gaba da gudanar da ziyarar aiki a kasar Saudiyya domin ganawa da mahukuntan kasar da nufin tattauna batun hanyar dawo da dukkanin ‘yan ksar da suka rasa rayukansu a hatsarin Mina zuwa ga iyalansu tare da ganawa da tawagar likitocin Iran da suke kula da lafiyar mahajjatan kasar a lokacin aikin hajji gami da zagaya asibitocin da aka kwantar da Iraniyawan da hatsarin na Mina ya ritsa da su domin duba lafiyarsu.



3381780

Abubuwan Da Ya Shafa: mina
captcha