IQNA

Haramtacciyar Kasar Isra’ila Za Ta Shirya Gasar Kur’ani Da Hadisi

18:41 - October 06, 2015
Lambar Labari: 3382525
Bangaren kasa da gasa, haramtacciyar kasar Isra’ila na shirin gudanar da wata gasa ta kur’ani da hadisi a cikin wannan mako da nufin kara yada al’and larabawa.

Kamfanin dillanicn labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bawabah News cewa, a daidai lokacin da haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a cikin yankunan palastinawa da ke gabar yammada kogoon jodan, tana shirin shirya gasar kur’ani da hadisi.
A irin wannan lokacin majiyoyin Palasdinawa sun yi gargadi kan karin tabarbarewar al'amura a Palasdinu sakamakon tsananta kai hare-haren wuce gona da iri kan yankunan Palasdinawa da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila gami da tsagerun yahudawan sahayoniyya suke yi, inda a cikin sa'o'i ashirin da hudu  kacal Palasdinawa uku suka yi shahada wasu daruruwa kuma suka jikkata.

 

Kungiyar bada agajin gaggawa ta palasdinu a jiya Litinin ta yi gargadi kan karin tabarbarewar al'amura musamman a yankunan da suke gabar yammacin kogin Jordan da birnin da kewaye sakamakon tsananta kai hare-haren wuce gona da iri da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila gami da tsagerun yahudawan sahayoniyya suke yi kan alasdinawa

Dangane da gasar da yahudawan ke shirin shiryawa kuwa, mutane 4 suka kai ga mataki na karshe kuma gidan radio Isra’ila ne zai watsa shirin gasar gasar kai tsaye, da nufin abin da suka kira kara alaka da al’adun larabawa da musulmi.

 

3382156

Abubuwan Da Ya Shafa: HKI
captcha