Kamfanin dillanicn labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na afrigatenews.net cewa, wasu daga cikin kungiyoyi da cibiyoyi masu gwagwarmaya a fagen siyasa akasar Moroco sun nuna rashin amincewa da wata ziyara da aka shira ga Muhamamd Uraifi malamin wahabiya zuwa Moroco.
Muhamamd Uraifi dai sanannen mutum a tsakanin dukanin masu bina bubuwa da suke wakana a cikin kasashen larabawa, wanda yake taka gagarumar rawa a fagen yada akidar kafirta musulmi da ta samo asali da mummunar akidar nan ta wahabiyanci.
Ya kasancea asahun gaba wajen yada akidoji na kafirta musulmi da rarrab akan muslmi a duk inda suke, kamar yada kuma ya kasancea sahun gaba wajen ingiza matasan larabawa donin shiga cikin kungiyoyin ta’addanci na duniya.
Uraifi dan kasar saudiyya ne wanda yke bin koyarwar irin wadda kasar take tafiya a kanta ta wahabiyanci, duk kuwa da cewa shi yana da tsatsauran ra’ayi, ta yadda hatta giggan wahabiyawa sukan yi sabani da shi saboda abubuwan da yake yi na rashin lissafi da sunan wahabiyancin.
Daga cikina bubuwan da Uraifi ya yin a ban mamakia cikin lokutan da suka gabata, shi ne fitar da fatawar halastawa yan ta’adda yin auren wucin gadi na ‘yan saoi, ta yadda mace za ta iya auren yan ta’’ada da dama a rana guda, a matsayin nata gudunmawar jihadi.
3383577