Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar da ke kula da harkokin hubbaren Hussaini cewa, an gudanar da taron canja tutoci a hubbarorin Imam Hussai (AS) da kuma Abbas (AS) masu tsarki a birnin Karbala mai alfarma kamar dai yadda aka saba.
A kowace shekara a daidai irin wanann lokaci ana gudanar da bikin canja tutoci na wadannan hubbarori biyu na Imam Hussain (AS) da kuma Abul Fadhl Abbas (AS) da suke a birnin mai alfarma, a lokacin da ake shiga lokacin fara makokin shahadarsu amincin Allah ya tabbata a gare su.
Dubban mutanen ne suke taruwav alokacin da ake gudanar da wannan taro na canja tutocina wannan wuri mai tsarki, haka nan kuma aka gabar da taken na nuna mika wuya ga imam wanda Allah madaukakin sarki ya farlanta biyayya gare shi.
Iamar dai yadda aka saba akan cire tuta mai launin ja da ke kan kubbar wadannan hubbarori biyu masu tsarki, akan maye gurbinsu da tutoci biyu masu launin baki, domin nuna bakin ciki da shiga wannan lokaci na tunawa da shahadarsu.
A nasu bangaren jami’an tsaro sun dauki kwararan matakai na kare mahalarta wannan wuri domin kauce wa faruwar ayyukan ta’addanci daga yan ta’adda kamar yadda sukan a yi a wasu lokuta.
3385730