IQNA

Kungiyar Kasashen Musulmi Ta Yi Kira Da A Kare Musulmin Afirka Ta Tsakiya

22:01 - October 18, 2015
Lambar Labari: 3388696
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kasashen musulmi ta yi kira ga majalisar dinkin duniya da ta kare mabiya addinin muslinci a kasar jamhuriyar Afirka ta tsakiya.


Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, Tijani Gadiyo manzon musamman na kungiyar kasashen musulmi a jamhuriyar Afirka ta tsakiya ya yi kira ga majalisar dinkin duniya da ta kare mabiya addinin muslinci a kasar jamhuriyar Afirka ta tsakiya daga mabiya addinin kirista masu tsatsauran ra’ayi da ke kashe su.

Gwamnatin rikon kwarya ta Jamhuriyar Afirka ta tsakiya ta sanar da makoki na tsawon kwanaki uku dangane da kisan mutane kimanin arbain  da aka yi a kasar a cikin kwanakin nan.



Shugabar rikon kwarya ta kasar ce ta sanar da domin juyayi kana bin da ya faru na kisan mutane 40 a kasar sakamakon rikin da ya sake gocewa a kasar a cikin ‘yan kwanakin nan, wanda kungiyoyin farar hula da dama suna gudanar da zanga-zanga a kasar tare da yin kira ga shugabar  da safka daga kan shugaban kasar sakamakon kasa shawo kan lamurra a kasar.



A ranar ashirin da shida ga watan Satumban da ya gabata ne dai aka kashe wani matashi musulmi a birnin Bangui fadar mulkin kasar, tare da cire kansa da kuma yin rubutun izgili ga musulmi da jininsa  akan gawarsa, lamarin da ya sak ejawo wani tashin hankali a birni.



3386341

Abubuwan Da Ya Shafa: oic
captcha