IQNA

Wani Kirista Ya Halarci Taron Juyayin Shahadar Imam Hussain (AS) A Kasar Amurka

18:52 - October 23, 2015
Lambar Labari: 3392952
Bangaren kasa da kasa, Mike wani kirista ne dan kasar Amurka wanda ya halarci taron juyayyin shahadar Imam Hussain (AS) a birnin Detroit na kasar Amurka.


Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dilalncin labaran kasar Iraki NUN cewa, Mike dan kasar Amurka ne kirista wanda ya halarci taron juyayyin shahadar Imam Hussain (AS) a birnin Detroit na kasar.

Shi dai dan shekaru 45 ne da haihuwa, wanda ya bayyana lamarin Imam Hussain (AS) da cewa lamari ne wanda ya shafi dukaknin ‘yan adam baki daya, kuma raya lamarinsa raya lamarin ‘yan adamtaka ne.

Mike ya shiga cikin mabiya tafarkin shi’a a birnin Detroit, inda ake gudanar da tarukan juyayin shahadar Imam Hussain (AS) tare da iyalan gidan manzon, da hakan ya hada da bugun kieji da ake domin nuna bakin ciki kan hakan.

Ya ci gaba da cewa Imam Hussain (AS) ya yi sadaukantarwa da rayuwarsa da iyalansa da masoyansa domin kawai ya ga a adalci ya wanzu a tsakanin bil adama, a kan haka wannan ya tababtar da cewa shi mutum ne na musamman a tsakanin bil adama.

Dangane da abin da ya faru da shi wajn kokarin kare gaskiya da kuma yaki da karya da bata ya rasa ransa, wanda hakan ke nufin cewa shi ya yi shahada  akan tafarkin gaskiya, kuma hakan ne yasa shi zama mai matukar kaunar Hussain (AS) a cikin rayuwarsa.

3392861

Abubuwan Da Ya Shafa: ashura
captcha