Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafukan sadarwa na yanar gizo na kafofin yada labaran Iraki cewa, miliyoyin mutane suna ci gaba da isa birnin Karbala mai alfarma.
Bayanin ya ci gaba da cewa kamar kowace shekara miliyoyin mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ne suke ci gaba da isa wannan wuri mai alfarma domin raya wannan babbar rana.
Ana su bangaren jami’an tsaron kasar Iraki sun dauki tsauarar matakai domin kare miliyoyin musulmi da suke gudanar da irin wadannan ayyuka na ziyara a wannan wuri mai tsarki, tare da gudanar da tarukan wayar da kai da ilmantarwa kan wannan tafarki.
Shahada da jikaktar Mutane 23 masu ziyarar Imam Hussain
Rahotanni sun ce mutane 23 ne suka yi shahada ko suka jikkata sakamakon hare-haren kunar bakin waken da aka kai kan tawagar masu ziyara a Karkuk da kuma gabacin gundumar Salhuddin.
Kamfanin dilalncin labaran Saumaria News ya bayar da rahoton cewa, wani dan kuna bakin waken ya tayar da wasu bama-baman ne a kan masu tafiya da suke kan hanyarsu ta zuwa wurin ziyara a yankin Tozkhormato.
Bayan kai harin an tabbatar da mutuwar mutuwar mutane kimanin 20 a wurin da suka yi shahada a nan take, yayin da wasu kuma suka jikkata.
A daya bangaren kuma kamfanin dillancin labaran Sky News ya habarta cewa, wani harin da aka kai kan masu tafiya zwa wajen ziyarar a wasu yankuna mutane kimanin 23 sun yi shahada.
3392852