Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sumar News cewa, Walid Bin Talal dan gidamn sarautar Al Saud ya bukaci da akafa wani kawance tsakanin Isra’ila da Saudiyya domin yaki da Iran.
Walid ya bayyana hakan ne a matsayin mafificiyar hanya domin kawo karshen abin da yak ekira kutsen Iran a cikin harkokin kasashen larabawa, da kuma yadda ta zama babban karfen kafa ga kasarsa a hankoronta na fadada ikonta.
Ya ci gaba da cewa babu wata kasa wadda take a matsayin barazana ga Saudiyay da Isra’ila a halin yanzu kamar kasar Iran, a hakn ya ce ya zama wajabi a kafa irin wannan kawance domin takushe kaifin samuwar Iran da kuma karbuwarta a yanin gabas ta tsakiya.
Walid Bin talal dai dan gidan sarautar Saudiyya ne da ya shahara a duniya wajen yawan dukiya, saboda kasuwancin da yake a cikin kasashen larabawa da kuma kasashen yammacin turai, wanda hakan ya ba shi damar zama babban biloniya.
Haka nan kuma yana amfani da kudaden nasa wajen bushsha a kasashen turai da caca da kuma daukar nauyin tarukan alfasha a ciki da wajen kasar ta Saudiyyah, tare da shirya fati domin yin masha’a da izgili da kuma barnata dukiyar.
Ya ce suna hankoron ganin sun murkushe intifadar Palastine, da kuma dakile duk wani yunkurin ganin an yi Allawadai da Isra’ila, domin kuwa a halin yanzu akwai bukatar hada kai tsakanin larabawa da Isra’ila, domin tunkarar Iran.
3409336